An Tsige DPO Daga Kujerarsa Bayan Sheke Wanda Ake Zargi da Farmakar Fasto Sulaiman

An Tsige DPO Daga Kujerarsa Bayan Sheke Wanda Ake Zargi da Farmakar Fasto Sulaiman

  • Kwamishinan 'yan sanda ya tsige wani DPO daga kujerarsa bisa zargin sheke mai laifin da aka kame kan hannu a farmakin da aka kai kan fasto Johnson Suleiman
  • An kai farmaki kan fitaccen fasto a Najeriya, lamarin da ya tada hankalin jama'a da dama a kasar nan
  • An kamo wasu mutanen da ake zargin sun aikata laifin, kuma ana ci gaba da bincike kan abin da ya faru

Jihar Edo - Kwamishinan 'yan sandan jihar Edo, AIG Abutu Yaro ya cire DPO na yankin Auchi, CSP Ayodele Suleiman daga kujerarsa bisa laifin kashe wanda ake zargin da aka kama kan kai farmaki a tawagar fasto Johnson Suleiman, mai kula da cocin Omega Fire Ministry.

Hakazalika, an umarci jami'in da ya gaggauta mika kansa ga hukumar 'yan sanda domin ba da bahasi kan abin da ya faru, rahoton Punch.

An tsige DPO daga matsayinsa bisa zargin kashe wanda ya farmaki fasto Suleiman
An Tsige DPO Daga Kujerarsa Bayan Sheke Wanda Ake Zargi da Farmakar Fasto Sulaiman | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da mai taimakawa kakakin hukumar na jihar, Jennifer Iwegbu ta fitar, ta ce, cire DPOn na daga matakan gano dalilan da suka kai ga mutuwar daya daga wadanda suka farmaki ayarin faston.

A cewar sanarwar:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"CP mai barin gado, wanda yanzu yake AIG Abutu Yaro ya umarci cire CSP Ayodele Suleiman, DPO na Auchi domin yin bayani hedkwatar jiha cikin gaggawa."

Sanarwar ta shawarci jama'ar gari da su kwantar da hankula kuma su yi hakuri, tare da tabbatar musu cewa, babu abin da zai hana a tono gaskiya duk inda ta shiga game da lamarin.

Yadda aka kama wadanda suka farmaki fasto Suleiman

Idan baku manta ba, jim kadan bayan samun labarin farmakar faston, an sanar da kama wasu mutanen da ake zargi da aikata mummunan aikin.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa, 'yan banga ne suka kama mutanen da ake zargin kana suka mika su ga 'yan sanda, daga nan ne kuma aka kashe daya daga cikinsu.

Bayan samun labarin kashe wanda ake zargin, fasto Suleiman ya yi rubutu a Twitter tare da zargin 'yan sanda na kokarin boye hujja game da harin da aka kai masa.

An ruwaito cewa, faston ya kasance a kasar Tanzania tare da iyalansa, kuma an farmake shi ne a hanyar da komawa Auchi a ranar Juma'a 21 ga watan Oktoba.

An naqalto cewa, akalla mutane bakwai ne na kusa da faston suka rasa rayukansu a wannan mummunan harin.

Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Motoccin Babban Malamin Addinin Nigeria Hari, Sun Kashe Mutum 7 Har Da Yan Sanda

A wani labarin, yan bindiga sun kai wa ayarin motoccin Apostle Johnson Suleiman hari a kanyar Benin-Auchi, Jihar Edo, a ranar Juma'a sun kashe mutum bakwai ciki har da yan sanda uku.

The Punch ta tattaro cewa Suleiman ya dawo daga tafiya ne a kasar waje yana hanyarsa ta zuwa Jihar Edo inda yan bindigan suka kai masa hari a kusa da Auchi a jihar.

Yayin harin, yan bindigan, an rahoto sun bude wa ayarin motoccin wuta, sun kashe yan sanda uku masu tsaronsa da wasu mutane hudu da ba a gano su wanene ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel