Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

  • Gwamna Duoye Diri na Jihar Bayelsa ya kai ziyarar karamar hukumar Ogbia ta jiharsa don jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa
  • Diri, ya bawa mutane garin hakuri tare da musu alkawarin cewa za a kawo musu kayan tallafi game da iftila'in da ya same su
  • Gwamna Diri ya kara da cewa ambaliyar ruwar ta cinye gidan tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan da ke Otuoke hakan yasa ya kira shi dan gudun hijira a yanzu

Bayelsa - Ambaliyar ruwa da ke adabar jihar Bayelsa da wasu sassan Najeriya ya cinye gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ke Otuoke, Daily Trust ta rahoto.

Otuoke a karamar hukumar Obgia ce garin su tsohon shugaban kasar Najeriya.

Gwamna Diri
Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Tinubu ya yi magana mai girma game da bashin da ake bin Najeriya

Da ya ke magana yayin da ya ziyarci garin a ranar Juma'a, Gwamna Duoye Diri ya koka kan barnar da abin da ya kira "Iftila'i" ya yi wa rayuwar yan Bayelsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya jadada cewa garin Otuoke, wacce ke da Jami'ar Tarayya ta cika da ruwa kuma mafi yawancin mutanen sun bar muhallinsu, har da Jonathan.

Gwamnan ya bukaci mutanen kada su karaya yana mai cewa gwamnatinsa ta yi tanadin tallafa musu da kayayyaki don rage radadi.

Ruwa ta cinye gidan Jonathan da Jami'ar Tarayya a Otuoke, Diri

Wani sashi na jawabinsa:

"Kamar yadda kuka gani a wasu kananan hukumomi a jihar, mun zo Ogbia da kudancin Ijawa. Na tafi Ayama-Ijaw da Azikoro a Yenagoa.
"Yanzu na zo Ogba, gidan tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan. Kun ga irin asarar da ka yi a Otuoke. Ruwan ya yi karfi tamkar rafi ne nan.

Kara karanta wannan

Yanzu Haka: Buhari Ya Karrama Jonathan, Wike Da Wasu Mutum 42 Da Lambar Yabo

"Wannan shine abin da na rika cewa. Iftila'i ya fada wa Bayelsa. Ruwa ya mamaye gidan tsohon shugaban kasar mu baki daya. A nan ne akwai jami'ar tarayya. Hakan ya sa tsohon shugaban kasar ya zama IDP."

Nima Ban Tsira Ba: Wani Gwamnan Najeriya Ya Ce Ambaliyar Ruwa Ta Ci Gidansa

Tunda farko, Gwamna Douye Diri na Jihar Bayelsa ya koka cewa ambaliyar ruwa da ya shafi sassan jihar ta ci gidansa na kansa da ke Sampou a karamar hukumar Kolokuma/Opokuma a jihar.

Diri, wanda ya yi rangadin duba irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a wasu garuruwa ya koka kan wahalhalun da ambaliyar ya jefa mutane ciki, Daily Trust ta rahoto.

Gwamnan ya samu rakiyar kwamishinan muhalli kuma shugaban hukumar kula da ambaliya, Eselema Gbaranbiri, takwaransa na ma'aikatar ayyuka, Moses Teibowei, da Ayibaina Duba da wasu manyan jami'an gwamnati, sun ziyarci garuruwan da ambaliyar ta shafa ciki har da Tungo, Sagabama da Adagbabiri duk a karamar hukumar Sagbama.

Kara karanta wannan

An Samu Jihar Farko a Arewa da ta fara Cin Dukiyar Fetur Bayan Gano Danyen Mai

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel