Najeriya na Kukan Kudi, NNPC Ya Kashe Naira Biliyan 780 a Albashi da Shakatawa

Najeriya na Kukan Kudi, NNPC Ya Kashe Naira Biliyan 780 a Albashi da Shakatawa

  • Binciken kudin da aka gudanar, ya nuna kamfanin NNPC ya kashe Naira biliyan 780 a shekarar 2021
  • N7.5bn sun tafi wajen samar da tsaro, sannan an batar da N2.7bn domin a biya haya, N15bn a zirga-zirga
  • Abin da aka kashe da sunan biyan albashi da horas da ma’aikata a wancan shekarar ya haura N400bn

Abuja - Kudin da kamfanin NNPC ya batar a shekarar bara ya kai Naira biliyan 788.7, akasin Naira biliyan 648.6 da aka kashe a shekarar 2020 kafin ta.

A wani rahoto da Daily Trust ta fitar a makon nan, an fahimci a 2020 kamfanin man ya karar da Naira biliyan 388.4 wajen biya ma’aikatansa albashi.

Binciken kudin da aka gudanar ya tabbatar da cewa fanshon da aka biya ya kai Naira biliyan 150.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Fadawa MTN, Glo, Airtel Su Dakata da Karin Farashin Da Suka Yi a Boye

Rahoton ya kuma nuna fiye da Naira biliyan 80 sun tafi wajen canjin Naira da kudin waje. Abin da aka kashe a kan wannan a 2020, bai wuce N42bn ba.

Shakatawa da katin waya sun ci N26bn

Ba a nan kurum binciken ya tsaya ba, an fahimci ma’aikatan NNPC a Najeriya sun batar da Naira biliyan 11 wajen shakatawa a shekarar da ta gabata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wajen biyan kudin aikin lauyoyi da sauran kwararru, kamfanin ya rasa Naira biliyan 46. Kudin katin waya kuwa ya zuke Naira biliyan 15 a 2021.

Shugaban NNPC
Shugaban kamfanin NNPC Hoto: @nnpclimited
Asali: Twitter

Darektocin da ke rike da kamfanin kasar sun yi sanadiyyar kashe Naira miliyan 390. A harkar tafiye-tafiye kuwa, kimanin Naira biliyan 10 suka yi ciwo.

Nawa NNPC ta samu a shekarar?

Jaridar Solacebase tace duka-duka abin da kamfanin kasar ya samu a shekarar ya zarce Naira tiriliyan 6.4, hakan ya zarce abin da aka samu a shekarar baya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnati Ta Tanadi N470bn Don Karawa Malaman Jami'a Albashi Da Gyara Jami'a

Daga kudin da aka samu, ma’aikatan na NNPC sun batar da Naira tiriliyan 5.3. Sai dai kamfanin zai bugi kirji, yace har ya iya samu ribar Naira biliyan 674 a baran.

Rahoton ya nuna awatanni 12, an kashe N1.9bn a wajen dab’i da sayen kayan aikin ofis.

Sha’anin tsaro da horas da ma’aikata sun ci Naira biliyan 7.5 da kuma Naira biliyan 12 a shekarar bara, NNPC ya kashe wasu Naira biliyan 2.7 a biyan kudin haya.

An samu fetur a Arewa

A makon nan aka ji labari, Mai girma Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya shaidawa Duniya cewa sun shiga sahun Jihohin Neja-Delta masu arzikin man fetur.

A kowane wata, Gwamnatin jihar Kogi za ta rika karbar karin 13% daga kason FAAC saboda rijiyar Ibaji ya fara kawowa Najeriya kudi, a karon farko a Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel