Abuja: Kyakyawar Budurwa Ta Tashi Saurayi Mai Katuwar Mota, Ta Bashi Lambar Wayarta

Abuja: Kyakyawar Budurwa Ta Tashi Saurayi Mai Katuwar Mota, Ta Bashi Lambar Wayarta

  • Wata dirarriya kuma kyakyawar budurwa ta tashi namiji yayin da ta ci karo da kyakyawan mutum ba motarsa a Abuja
  • Fidelis Ozuawala ya bayyana yadda budurwar da bai sani ba ta ajiye masa lambar wayarta a kan motarsa bayan ta rubuta a takardar tsire
  • Ya sanar da Legit.ng cewa daga nan bai san inda budurwar tayi ba kuma labarinsa ya janyo maganganun jama’a a Facebook

FCT, Abuja - Fidelis Ozuawala ya bayyana hoton wata takarda da budurwar ta fada soyayyarsa ta rubuta masa a yayin da suka ci karo a cikin jama’a.

Budurwa a Abuja
Abuja: Kyakyawar Budurwa Ta Tashi Saurayi Mai Katuwar Mota, Ta Bashi Lambar Wayarta. Hoto daga Fidelis Ozuawala
Asali: Facebook

Kamar yadda Fidelis ya bayyana, dukkan lamarin ya faru ne a Abuja yayin da ya ajiye motarsa kuma ya fita daga cikinta.

Kara karanta wannan

APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna

Budurwar ta rubuta lambar wayarta a kan wata takarda da tayi kama da ta tsire kuma ta ajiyeta a wurin kofar motar Fidelis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta yi rubutun tsaf sannan ta cika bujen ta da iska.

“Barka, sunana Lisa. Ina gefen wurin wankan nan yayin da na ganka. Don Allah ka kira ni.”

A yayin zantawa da Legit.ng a gajeruwar hira, Fidelis yace lamarin ya faru a yankin Gwarimpa dake babban birnin tarayya a Abuja.

“Ina kokarin bude kofa ne na taba wata takarda, na bude ta kuma na ga sako ne daga wata budurwa.”

- Yace.

Tun farko a shafinsa na Facebook ya rubuta labarin mai bada dariya:

“‘Yan matan Abuja na tashin maza. Na ga wannan a bangaren kofar direba a mota ta.
“‘Yan mata a dauka wannan salon, ba abu ne mara kyau ba. Abun ya birge kuma zai iya yuwuwa abu ne da za a dinga tunawa, amma fa idan kin ci karo da matashin da bashi da mata.”

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet, Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

Ma’abota amfani da Facebook sun yi martani

Charles Uchechi Nwaokonko yace:

“Abun dariya, zasu iya tashin matashin da suka ga dai da kudi tare da shi.”

Queen Winnie tayi tsokaci da:

“Wannan karfin halin nata ya birge ni. Babu wani aibu kan abinda tayi. Ta ga abinda take so ne kuma ta bi shi.”

Hatta Mijina Yana Alfahari dani: Mahaifiyar Yara 2 Direban Tasi Ta Birge Jama’a a Bidiyo

A wani labari na daban, Matar aure kuma mahaifiyar yara biyu wacce direban tasi ce wacce ta shawarci sauran mata da kada su saki jiki ba tare da neman na kansu ba.

Kemi Toriola wacce mahaifiyar yara biyu ce ta shiga sana’ar tukin tasi bayan annobar COVID-19 ya yi matukar illa ga kasuwancinta.

Kemi mai shekaru 35 tace tana da cikakken goyon bayan mijinta tunda shine ya taimaka mata ta samu mota wacce zata dinga biyan kudin a hankali har ta zama mallakinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel