Kogi: Ana Tsaka da Rikici da Dangote, Yahaya Bello Yayi wa BUA Kiran Gaggawa

Kogi: Ana Tsaka da Rikici da Dangote, Yahaya Bello Yayi wa BUA Kiran Gaggawa

  • Majalisar jihar Kogi tayi wa kamfanin simintin BUA kiran gaggawa yayin da yake tsaka da rikici har da zuwa kotu da kamfanin simintin Dangote dake Obajana
  • Majalisar na tuhumar kamfanin BUA kan mallake fili mai girman kadada 50,000 na jama’ar jihar ba tare da biyansu ko sisin kwabo ba tun 2012
  • Majalisar ta yi kira ga kamfanin da su zo su kare kansu ko kuma ta janye satifiket din mallakar filayen da kamfanin yayi tun shekaru 10 da suka gabata

Kogi - Majalisar jihar Kogi ta yi kiran gaggawa ga kamfanin siminti na BUA kan fili mai girman kadada 50,000 da ake zargin ta siya shekaru 10 da suka gabata amma har yanzu kamfanin bai biya kudin ba.

Gwamna Yahaya Bello
Kogi: Ana Tsaka da Rikici da Dangote, Yahaya Bello Yayi wa BUA Kiran Gaggawa. Hoto daga punchng.com
Asali: Facebook

Wannan cigaban ba zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ke tsaka da cashewa da kamfanin Dangote kan rikicin mallakar kamfanin siminti na Obajana.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gwamnatin Buhari ta gani makarantun bogi 349 a jihar Arewa dake cinye kudin ciyar da dalibai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin yanzu suna gaban kotu bayan duk kokarin da aka yi na shawo kan matsalar ya ci tura.

A ranar Litinin, ‘yan majalisar jihar Kogi sun yi wa kamfanin BUA kiran gaggawa domin tattaunawa da su wanda aka yi a wani otal dake Lokoja, babban birnin jihar Kogi, jaridar Daily Trust ta rahoto.

An dakatar da al’amura a zauren majalisar jihar tun bayan da ibtila’in gobara ya fadawa majalisar a ranar Litinin da ta gabata.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Mataimakin kakakin majalisar jihar, Alfa Momoh Rabiu, wanda ya jagoranci sammacin bayan ya saurari bayani daga mukaddashin sobeyo janar na jihar, Salisu Mustapha, ya bayyana mamakinsa kan hallayar da kamfanin BUA din ya nuna.

“Muna da matsala da kamfanin BUA kan fili mai girman kadada 50,000 da suka samu a 2012 kuma har suka samu satifiket din mallaka amma har yanzu basu biya ko sisin kobo ba. Mun rubuta wasika zuwa ga kamfanin sau da yawa amma har yanzu bata yi martani kan ko daya daga cikin wasikarmu ba.

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

“Basu biya ko ficika ba ga al’ummomin da suka mallaki filayen.”

- Salihu Mustapha yace.

Umar Tanimu, shugaban kwamitin wucin-gadin yace babban laifi ne da kamfanin BUA din suka tafka na rike filayen tsawon shekaru 10 ba tare da sun biya jama’a hakkinsu ba.

Ya kamata a kira kamfanin su zo su yi bayanin dalilin da ya hana su biyan kudin filayen da kuma rashin sauke hakkin al’ummomin da abun ya shafa, yace.

Ya kara da cewa, idan kamfanin BUA ya ki biyan kudin filayen jama’a da abun ya shafa, gwamnati zata kwace satifiket din shaidar mallakarsu.

A yayin da aka tuntubi Sunday Ogieva, jami’an sadarwa na kamfanin BUA, yace ba zai iya tsokaci kan lamarin ba.

FG Tayi Umarnin Bude Kamfanin Simintin Dangote dake Kogi

A wani labari na daban, Gwamnatin Najeriya tayi umarnin sake bude kamfanin simintin Dangote dake Obajana a jihar Kogi.

Gwamnatin ta kara da bada umarnin cewa, dukkan wasu matsaloli dole ne a shawo kansu a shari’ance, TVC News suka rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel