Da Duminsa: FG Tayi Umarnin Bude Kamfanin Simintin Dangote dake Kogi

Da Duminsa: FG Tayi Umarnin Bude Kamfanin Simintin Dangote dake Kogi

  • Gwamnatin tarayya tayi umarnin bude kamfanin simintin Dangote dake Obajana wanda Gwamna Yahaya Bello ya garkame
  • Gwamnatin bata tsaya a nan ba, ta kara da umarnin cewa duk wata matsala a garzaya gaban kotu domin shawo kanta a shari’ance
  • Tun dai a makon da ya gabata ne ake ta kai ruwa rana tsakanin Gwamnatin jihar Kogi da Alhaji Aliko Dangote kan rikicin mallakin kamfanin

Gwamnatin Najeriya tayi umarnin sake bude kamfanin simintin Dangote dake Obajana a jihar Kogi.

Gwamnatin ta kara da bada umarnin cewa, dukkan wasu matsaloli dole ne a shawo kansu a shari’ance, TVC News suka rahoto.

Dantgote Cement
Da Duminsa: FG Tayi Umarnin Bude Kamfanin Simintin Dangote dake Kogi. Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da fadar shugaban kasa ta shiga tsakanin rikicin da ya barka tsakanin Alhaji Aliko Dangote da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi kan mallakar kamfanin.

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Kashe Saurayinta Da Wuka Cikin Dare Kusa Da Dakin Hotel

Wannan rikicin ya janyo rufe kamfanin wanda gwamnatin ta umarci ‘yan sa kai yi hakan kan karantsaye ga dokar haraji.

Taron da aka yi a fadar shugaban kasa kuma Dangote, Gwamna Yahaya Bello da Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa suka samu halarta.

Sai dai hukumar kamfanin Dangote tace sun kammala shirin tunkarar kotu domin shawo kan lamarin a shari’ance.

Manajan Daraktan kamfanin siminti na Dangote, Michael Pucheros a wata takarda da ya fitar ya sanar da cewa kamfanin siminti na Dangote mallakinsu ne.

A yayin da aka yi niyyar rufe kamfanin da karfi da yaji, ‘yan da kai sun harba ma’aikatan kamfanin 27 tare da lalata wasu daga cikin kayayyakin kamfanin.

Rikicin Mallaka: Dangote da Yahaya Bello Sun Gurfana a Fadar Buhari Za a Yi Musu Sasanci

A wani labari na daban, Alhaji Aliko Dangote, shugaban kamfanonin Dangote a ranar Litinin ya halarci wata ganawa tare da Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba

Taron wanda ya samu halartar Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa an yi shi ne domin rikicin mallakin kamfanin simintin Dangote dake Obajana a jihar Kogi, jaridar TheCable ta rahoto.

TheCable ta gano cewa an fara taron ne da karfe hudu na yammacin ranar Litinin.

Wannan cigaban na zuwa ne bayan kwanaki da majalisar jihar Kogi tayi umarnin rufe kamfanin Dangote bayan asalin 'yan yankin sun tada balli kan batun mallakar kamfanin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel