‘Yan Bindiga Sun Budewa Masu Bauta Wuta, Sun Halaka 2 tara da Jigata Wasu a Kogi

‘Yan Bindiga Sun Budewa Masu Bauta Wuta, Sun Halaka 2 tara da Jigata Wasu a Kogi

  • Miyagun ‘yan bindiga sun kai mummunan farmakin cocin Celestial dake Falele a garin Lokoja na jihar Kogi
  • ’Yan bindigan sun halaka mutum biyu yayin da suka budewa masu bauta wuta a ranar Lahadi da yammaci
  • Daga isar su suka budewa jama’a wuta inda masu bauta suka fara gudun ceton rai amma duk da haka sai da suka yi barna

Kogi - ‘Yan bindiga sun kai farmaki cocin Celestial dake yankin Felele a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

‘Yan bindigan sun kai mummunan harin ne da yammacin Lahadi, kamar yadda jaridar TheCable ta rahoto.

Cocin Kogi
‘Yan Bindiga Sun Budewa Masu Bauta Wuta, Sun Halaka 2 tara da Jigata Wasu a Kogi. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

TheCable ta gano cewa ‘yan bindigan sun fara harbi babu sassauci yayin da suka shiga farfajiyar cocin.

Masu bai ta da yawa dake wurin sun fara gudun ceton rai a yayin da lamarin ke faruwa.

Kara karanta wannan

An Bindige Mutum 1, Wasu 18 Sun Jigata a Arangamar ‘Yan Daban PDP da APC a Zamfara

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutum biyu ne suka sheka lahira yayin da masu bauta da tarin yawa suka jigata.

Wadanda suka jigata tuni aka mika su cibiyar magani ta tarayya dake Lokoja don samun kular masana kiwon lafiya.

A yayin tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, William Aya, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi yace ‘yan sandan yankin Falele sun samu rahoton faruwar lamarin wurin karfe 7 na yamma.

Aya ya bayyana cewa Edward Egbuka,kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin fara bincike kan lamarin.

“Lamarin ya faru, mutum biyu an tabbatar da mutuwarsu, uku yanzu suna asibiti ana kula dasu.”

- Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ya tabbatar da hakan.

A baya-bayan nan, Kogi na fuskantar karuwar harin ‘yan bindiga a wuraren bauta, ofisoshin ‘yan sanda da sauran wuraren gwamnati.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Je Har Babban Masallaci, Sun Yi Awon Gaba da Wani Basarake a Arewacin Najeriya

A watan Augustan 2021, mambobin Living Faith Church Worldwide dake yankin Osara a karamar Hukumar Adavi aka sace a farfajiyar cocin.

A watan Satumban 2021, ‘yan bindiga sun halaka mambobin Evangelical Church Winning All tare da sace wasu mutum biyu a farmakin da suka kai cocin dake kan titin Kabba zuwa Okene.

Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Bankuna Uku, Sun Tafka Barna a Jihar Kogi

A wani labari na daban, wasu da ake zaton 'yan fashi da makami ne ɗauke da bindigu sun farmaki rassan bankuna uku, UBA, Zenith da kuma First Bank a yankin Ankpa, jihar Kogi, inda suka kwashi kuɗi iya son ransu.

Yan Fashin, adadin mutum 20, an ce sun shiga garin da misalin ƙarfe 2:00 na rana. Da farko suka farmaki bankin UBA, daga nan suka zarce Bankin Zenith, daga bisani suka mamaye First Bank.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng