Jerin Makarantun Sakandare Mafi Tsada A Najeriya, Zunzurutun Kudin Makaranta Da Ake Biya Ya Bayyana

Jerin Makarantun Sakandare Mafi Tsada A Najeriya, Zunzurutun Kudin Makaranta Da Ake Biya Ya Bayyana

Idan aka yi la'akari da kudin makaranta, bisa dukkan alamu akwai wasu makarantun sakandare a Najeriya da yaran masu matsakaicin karfi ba za su iya zuwa ba.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Mafi yawanci, idan ba duka ba a wannan matakin suna bin tsarin karatu na Birtaniya ne ko Amurka wadanda sune tsari na kasa da kasa da ya kunshi dukkan sauye-sauye na zamani a dukkan bangarorin rayuwa.

Daliban makarantan sakandare a Najeriya
Jerin Makarantun Sakandare Mafi Tsada A Najeriya. Hoto: @Nairametrics
Asali: Twitter

Daga sama zuwa kasa, ga makarantun:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. American International School Lagos (AISL)

An kafa ta a 1964, American International School Lagos ta fara daga ajin kananan yara (preschool) zuwa grade 12 inda daliban za su kammala da baban difloma ta Amurka, da zabin cigaba su samu difloma ta Baccalaureate na kasa da kasa.

Kara karanta wannan

Diyar Biloniya, Hauwa Indimi, Ta Koka Bayan Ta Siya Tumatir Din N8,000, Jama'a Sun Yi Martani

Daliban makarantan (fiye da 600) galibi yan Amurka ne, yayin da sauran sun hada da yan Birtaniya, Najeriya, Canada, Afirka ta Kudu, Israila, Lebanon, da Netherland. Sauran daliban sun fito daga kasashe daban-daban guda 50.

Kudin makaranta na kananan aji a zangon karatu na (2022/23) shine $28,049, manyan aji kuma $32,165.

2. British International School (BIS)

Makarantar tana Victoria Island a Legas kuma an kafa ta ne a 2001, BIS makaranta ce ta yan kasashe daban-daban kuma ta mata da maza, akwai masu kwana da jeka ka dawo daga shekara 11 zuwa 18.

BIS na daya daga cikin makarantu mafi tsada a Najeriya, yana bin tsarin koyarwa na Birtaniya inda ba a samun dalibai fiye da 20 a aji guda.

Ana shirya daliban don yin jarrabawar IGCSE da Advanced Level courses of Cambridge International Examinations (CIE).

Kudin makarantar yan jeka ka dawo shine N6.1 miliyan sannan masu kwana kuma N8.1 miliyan.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Na Hango N12bn Daga Sabon Harajin Motar da Tinubu Ya Kirkiro

3. Lekki International School

Makarantar ta yi fice a matsayin makarantar kwana irin ta Birtaniya na farko a Najeriya, an kafa ta ne a Satumban 2000 a Lekki Phase 1.

Manufar ta shine samar da yanayi inda dalibai za su gano kuma su habaka basirarsu.

Kudin makaranta na yan jeka ka dawo ya kai N4.6 miliyan duk shekara kuma masu kwana N6.8 duk shekara.

4. Grange School

An kafa makarantar a 1958 da manufar samar da ilimin irin na Birtaniya, ba don riba aka kafa makarantar ba, akwai dalibai mata da maza kuma akwai jeka ka dawo ne da masu kwana.

Makarantar tana Ikeja GRA, Legas Najeriya.

Akwai dalibai maza da mata 430 a bangaren frimare shekarunsu daga 4 zuwa 11. Sakandare kuma shekarunsu daga 7 zuwa 11 ko fiye, inda akwai dalibai 326.

Yan jeka ka dawo suna biyan N4.5 miliyan yayin da masu kwana suna biyan N6.5 miliyan duk shekara.

Kara karanta wannan

“Kamar a Fim”: Matashiya Ta Auri Hadadden Dan Koriya a Asiya, Hadadden Bidiyon Bikin Ya Zautar Da Yan Mata

5. Day Waterman College

An kafa kwalejin a shekarar 2008 a kauyen Asu kusa da Abeokuta, Jihar Ogun.

Daliban makarantar sun kai 500, shekarunsu kuma daga 11 zuwa 16.

Manufar makarantar shine tarbiyantar da yara da za su kawo canjin da ake bukata a kasa, shi yasa ake karfafa musu gwiwa su yi darrusa daban-daban.

Kudin makaranta shine N5.3 miliyan duk shekara kuma makarantar kwana ne zalla.

6. Meadow Hall School, Lagos

An kafa Meadow Hall a shekarar 2002 a unguwar Lekki II, makarantar mata da maza ne da ke gwamutsa tsarin karatun Birtaniya da Najeriya.

Kudin makarantar ya kai N3.2 miliyan ga masu jeka ka dawo su kuma masu kwana na su N5 miliyan.

Kudin makaranta: Daga N26, 000, Daliban KASU za su koma biyan N500, 000 a duk shekara

A wani rahoto, Jaridar FIJ ta ce masu biyan N24, 000 da N26, 000 a matsayin kudin karatu a shekara za su koma biyan N150, 000 da N500, 000, bayan karin da aka yi.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Daba Suka Caccaki Wani Dan Kasuwa Har Lahra a Jihar Kano

Wannan karin kudin makaranta da aka yi ya zo a lokacin da mutane ba su gama farfado wa daga annobar cutar COVID-19 da ta nakasa tattalin arziki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel