Kudin makaranta: Daga N26, 000, Daliban KASU za su koma biyan N500, 000 a duk shekara

Kudin makaranta: Daga N26, 000, Daliban KASU za su koma biyan N500, 000 a duk shekara

- Gwamnati ta yi karin da ya kusa kai 2000% a kan kudin makarantar KASU

- An kawo wannan karin ba a gama murmurewa daga annobar COVID-19 ba

- Masu kashe N100, 000 kafin su samu Digiri za su biya N300, 000 a shekara

An samu canjin kudin makaranta a jami’ar jihar Kaduna, inda wadanda su ka zo daga waje su ka gamu da tashin kusan 2000% a kan abin da su ke biya.

Jaridar FIJ ta ce masu biyan N24, 000 da N26, 000 a matsayin kudin karatu a shekara za su koma biyan N150, 000 da N500, 000, bayan karin da aka yi.

Wannan karin kudin makaranta da aka yi ya zo a lokacin da mutane ba su gama farfado wa daga annobar cutar COVID-19 da ta nakasa tattalin arziki ba.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai zai rushe kasuwar Panteka nan da mako 1

Shugaban sashen yada labarai na jami’ar KASU, Adamu Nuhu Bargo, ya yi bayanin abin da ya sa gwamnatin Kaduna ta dauki matakin kara kudin karatun.

Malam Adamu Bargo ya ce abin da jami’ar jihar ta ke samu a matsayin kudin shiga bai wuce N760m ba, don haka aka dauki matakin kara kudin karatu.

Bargo bai bayyana sabon farashin da aka sa ba, sai dai ya ce nan gaba za a fitar da cikakken bayani.

Wani tsohon shugaban kungiyar daliban Kaduna, Abdulrazak Shuaibu, ya tabbatar cewa daliban da su ka saba biyan N26, 000, za su koma biyan N150, 000.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun yi ram da mutane 240 cikin watanni 3 a Katsina

Kudin makaranta: Daga N26, 000, Daliban KASU za su koma biyan N500, 000 a duk shekara
Jami'ar jihar Kaduna
Asali: Twitter

Daliban gida da su ke karantar ilmin likitanci za su rika biyan N300, 000 bayan wannan kari da aka yi. Kafin yanzu N26, 000 su ke biya a kowace shekara.

Sauran daliban da su ka zo daga wata jiha za su koma biyan N500, 000 a shekara domin zama likitoci.

A lokacin da wasu dalibai su ke koka wa game da wannan kari, shugabannin jami’ar sun ce hakan zai taimaka wajen bada ilmi mai nagarta a jami’ar.

Kwanakin baya ne Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa da zarar ya kammala wa'adin mulkinsa zai bar jihar Kaduna.

Malam El-Rufai wanda ya shekara biyu ya na wa’adinsa na karshe a matsayin gwamna ya fadi haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidajen rediyon jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel