"Najeriya Na Cikin Halin Yaƙi", Sanatan APC Mai Ƙarfin Fada A Ji Ya Yi Magana Mai Ɗaukan Hankali

"Najeriya Na Cikin Halin Yaƙi", Sanatan APC Mai Ƙarfin Fada A Ji Ya Yi Magana Mai Ɗaukan Hankali

  • Orji Kalu, sanata mai wakiltan Abia ta arewa, ya ce Najeriya na filin daga ne saboda tana cin komai kuma bata sarrafa komai a matsayinta na kasa
  • Babban bulaliyar majalisar ya bayyana hakan ne yayin bita kan kasafin kudi na N20.5 tiriliyan da Shugaba Buhari ya gabatarwa majalisar a makon da ya wuce
  • Tsohon gwamnan na jihar Abia ya koka kan yadda tattalin arzikin kasar ke mutuwa kuma ya ce dole gwamnati ta rage kudaden da ta kashewa don nuna da gaske tana son ceto kasar

FCT, Abuja - Orji Kalu, sanata mai wakiltan Abia ta arewa kuma bulaliyar majalisa, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta rage kudaden da ta ke kashewa wurin gudanar da gwamnati kuma ta ceto kasar daga matsalar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Muna Shawaran Sake Ciwo Bashi Daga Wajen Asusun Lamunin Duniya, Ministar Kudi

A cewar Premium Times, tsohon gwamnan na Abia ya bayyana hakan ne yayin bita kan kasafin kudin 2023 a majalisa, yana mai cewa, "Najeriya na cikin halin yaki"

Orji Kalu.
Sanatan Kudu Mai Karfin Fada A Ji Ya Yi Magana Mai Ɗaukan Hankali, Ya Ce "Najeriya Na Cikin Halin Yaki". Hoto: Orji Uzor Kalu.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai ke cikin kasafin kudin 2023 na Buhari?

A ranar Juma'a, 7 ga watan Oktoba, Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na N20.5 tiriliyan ga majalisar tarayya.

Da ya ke magana kan abubuwan da ya lura da su a kasafin da aka gabatar, ya koka kan yadda tattalin arzikin kasar ke tabarbarewa.

Hakan na cikin wani bidiyo ne da sanatan ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 13 ga watan Oktoba.

Kalu ya ce dole gwamnati ta mayar da hankali don warware matsalar tattalin arziki a kasar.

Mene Najeriya ta ke samarwa?

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan Arewa Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Ya koka cewa Najeriya ba ta samar da komai amma tana cin komai a matsayin kasa.

Sanatan ya jadada cewa dole Najeriya ta koma noma idan mutanen kasar na son fitowa daga halin ni-'ya su da suka shiga.

Sanatan ya koka cewa gwamnati ba ta yin abin da ya dace don farfado da tattalin arziki da ke mutuwa kuma matatun mai sun dade ba su aiki.

Wani sashin na jawabinsa na cewa:

"Yaki muke yi a Najeriya... Babu wani abu da muke samarwa. Masan'antu sun mutu."

Orji Kalu ya ce yan takarar shugaban kasa na APC 9 na shirin janyewa, ya bayyana wanda za su marawa baya

A wani rahoton, shugaban masu tsawatarwa na majalisar dattawa, Orji Kalu, ya bayyana cewa yan takarar shugaban kasa tara daga jam’iyyar the All Progressives Congress (APC) na shirin janyewa daga tseren.

Kalu wanda bai ambaci sunayen masu takarar ba, ya bayyana cewa za su marawa kudirin shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan baya, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Yan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Da Suka Yi Rajista Da Satifiket Din WAEC/SSCE Kacal

Asali: Legit.ng

Online view pixel