Gobara Ta Kama Majalisar Dokokin Jihar Kogi a Yau Litinin

Gobara Ta Kama Majalisar Dokokin Jihar Kogi a Yau Litinin

  • Mun samu labarin cewa, majalisar dokokin jihar Kogi ta kama da wuta da safiyar yau Litinin 10 ga watan Oktoba
  • Ya zuwa yanzu dai ba a tabbatar da sanadiyyar tashin gobarar ba da kame farfajiyar majalisar da zaurukan zama
  • Ana yawan samun tashin gobara a bangarori daban-daban a Najeriya, lamarin da ke jawo asarar dukiya da rayuka

Jihar Kogi - Zauruka da farfajiyar majalisar dokokin jihar Kogi sun kama da wata gobara, inji wani rahoton Daily Trust.

Ya zuwa yanzu dai ba a san sanadiyyar kamawar wannan mummunan gobara ba da ta tashi a yau Litinin 10 ga watan Oktoba.

Gobara ta kone majalisar dokokin Kogi
Goba Ta Kama Majalisar Dokokin Jihar Kogi a Yau Litinin | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin majalisar dokokin jihar, Prince Mathew Kolawole ya shaidawa manema labarai cewa, hukumomi za su binciki lamarin.

Hakazalika, daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Salau Ozigi ya ce gobarar bata tsallaka zaurukan majalisar ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an tsaro a bakin majalisar sun shaidawa jaridar TheCable cewa, gobarar ta fara ne da misalin karfe 7 na safe.

Gobara ba za ta shafi zaman majalisa ba, inji kakaki

A bangare guda, kakakin majalisar jihar Kogi ya bayyana cewa, wannan gobarar ba za ta hana zaman da majalisar za ta yi ba, tare da cewa wutar bata lalata abubuwan dake da alaka da zauren ba.

A cewarsa:

"Mutanenmu na nan sun kira mu da safen nan. Za mu bar jami'an tsaro su yi aikinsu yadda ya dace.
"Wannan ba zai shafi zaman majalisa ba. Wutar bata shafi sandar majalisa ba kuma za mu iya zama a ko'ina domin yin aikinmu na zaman majalisa"

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana ko an samu asarar rayuka ba, amma hotunan da aka yada sun nuna irin asarar da aka tafka.

Najeriya Ba Za Ta Tsira Ba Idan Aka Zabi Shugaba Kamar Buhari a 2023, Inji Dattijon Arewa

A wani labarin, mai magana da yawun majalisar dattawan Arewa, Dakta Hakeem Baba-Ahmad ya bayyana cewa, bai dace Najeriya ta samu shugaba mai irin halayen Buhari ba, kuma dole shugaban Najeriya na gaba ya sha bamban da akidun Buhari.

Baba-Ahmad ya yi wannan tsokaci ne a wata tattaunawa da jaridar Punch da aka buga a ranar Lahadi 9 ga watan Oktoba.

Da yake koka yadda mulkin Buhari ya kasance, Baba-Ahmad ya ce:

“Bana tunanin za mu tsira na tsawon shekaru goma tare idan muka ci gaba da tafiya yadda muke a karkashin Buhari."

Asali: Legit.ng

Online view pixel