Najeriya Ba Za Ta Tsira Ba Idan Aka Zabi Shugaba Kamar Buhari a 2023, Inji Dattijon Arewa

Najeriya Ba Za Ta Tsira Ba Idan Aka Zabi Shugaba Kamar Buhari a 2023, Inji Dattijon Arewa

  • Dakta Hakeem Baba-Ahmad ya bayyana cewa, bai kamata Najeriya ta sake samun shugaban kasa irin Muhammadu Buhari na yanzu ba
  • Jigon daga dattawan Arewa ya zargi shugaba Buhari da bata shekaru tun daga 2015 zuwa yanzu ba tare da kawo wani sauyi ba
  • Ya yi tsokaci da cewa, idan aka zabi shugaba mai halaye irin na Buhari, to kasar nan ba za ta kai ga gaci ba

Mai magana da yawun majalisar dattawan Arewa, Dakta Hakeem Baba-Ahmad ya bayyana cewa, bai dace Najeriya ta samu shugaba mai irin halayen Buhari ba, kuma dole shugaban Najeriya na gaba ya sha bamban da akidun Buhari.

Baba-Ahmad ya yi wannan tsokaci ne a wata tattaunawa da jaridar Punch da aka buga a ranar Lahadi 9 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaba Goodluck ne alherin da Najeriya ta taba gani a tarihi, inji gwamnan Arewa

Buhari bai tsinana komai ba, inji dattijon Arewa
Najeriya ba za ta tsira ba idan aka zabi shugaba kamar Buhari a 2023, inji Dattijon Arewa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake koka yadda mulkin Buhari ya kasance, Baba-Ahmad ya ce:

“Bana tunanin za mu tsira na tsawon shekaru goma tare idan muka ci gaba da tafiya yadda muke a karkashin Buhari."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangare guda, ya bayyana tasirin matasa da jini a jika sabanin tsufa a tsakanin 'yan siyasa, inda yace kamata ya yi Najeriya ta duba mai jini a jika kuma mai tunanin gobe din gaje Buhari.

Ya shaidawa Punch cewa:

"Mutum zai iya zama matashi amma ya gaza yin komai, kuma mutum zai iya zamamai shekaru ya gaza gane menene sauyi. Ka duba shugaban kasa. Bai sauya komai ba tun daga 2015 har zuwa yau. To don haka ba zamu damu sosai game da shekaru ba, duk da hakan na da muhummanci."

Buhari Da Osinbajo Za Su Kashe N11.92bn Wajen Cin Abinci Da Zirga-Zirga

Kara karanta wannan

A Karon Farko, Wani Gwamnan Arewa Ya Bi Sahun Su Wike, Ya Nemi Shugaban PDP Na Kasa Ya Yi Murabus

A wani labarin, bincike ya nuna cewa, kasafin kudin 2023 da shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar a makon jiya ya bayyana adadin kudaden da ofishinsa da na mataimakinsa za su ci a fannin tafiya da abinci kadai ya zarce N11.92bn a shekarar.

Tafiye-tafiyen da ake nufi anan na cikin gida ne da wajen kasa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Jaridar Punch a yau Lahadi 9 ga watan Oktoba ta bayyana cewa, an ware N1.58bn domin kula da lafiyar jiragen sama, yayin da aka ware N1.60bn domin gyara injunan jiragen Gulfstream GV da CL605.

Asali: Legit.ng

Online view pixel