Allah Ya Yi Wa Ɗan Majalisar Katsina Rasuwa A Ƙasar Saudiyya

Allah Ya Yi Wa Ɗan Majalisar Katsina Rasuwa A Ƙasar Saudiyya

  • Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta samu labari masa dadi, bayan rasuwar daya daga cikin fitattun mambanta
  • Hakan na zuwa ne a yayin da mamba mai wakiltar karamar hukumar Bakori, Hon Dr Aminu Ibrahim Kurami ya rasu a kasar Saudiyya
  • Dan majalisar tarayyar ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya kuma ya bar matan aure biyu, yaya 11 da jikoki guda uku

Katsina - Dan majalisa mai wakilan karamar hukumar Bakori a majalisar dokokin jihar Katsina, Dr Ibrahim Aminu Kurami, ya rasu a Saudiya.

Dan majalisar ya tafi kasa mai tsarkin ne domin yin aikin Umrah, Daily Trust ta rahoto.

Dr Aminu Kurami
Allah Ya Yi Wa Ɗan Majalisar Katsina Rasuwa A Ƙasar Saudiyya. Hoto: Katsina Post
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

Menene sanadin rasuwar Dr Aminu Ibrahim Kurami

A cewar wata majiya daga yan uwansa, ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a Madina misalin ƙarfe 2 na dare lokacin Najeriya.

Ya rasu ya bar matan aure biyu, ƴaƴa 11 da jikoki guda uku.

An zabi Kurami ne matsayin dan majalisa a Katsina a zaben raba gardama da aka yi a ranar 31 ga watan Oktoban 2020, bayan rasuwar magabacinsa, Hon. AbdulRazaq Ismail Tsiga.

A lokacin da Daily Trust ta ziyarci gidan iyalan Kurami a ranar Litinin da safe, ta tarar da dandazon mutane da suka taho ta'aziyya.

Lakcaran Najeriya Ya Rasu A Cikin Motarsa Yayin Da Dalibai Ke Jiransa A Aji

Wani mai amfani da Facebook, Momodu Bameyi, ya yi alhinin rashin abokinsa, wani lackara, wanda ya rasu a cikin motarsa.

Bameyi ya bayyana cewa marigayin lakcaran yana da aji da zai koyar ne kuma ya tuka motarsa zuwa makaranta amma ya rasu a cikin motar.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Kwankwaso? An Bayyana Dan Takarar Da Ya Shirya Ceto Najeriya Idan Ya Gaji Buhari a 2023

An tattaro cewa daliban lakcaran sun jira shi a cikin aji amma ba su gan shi ba, hakan yasa suka tafi inda motarsa ya ke su duba ko me ke faruwa.

Sun isa wurin da motarsa ya ke don tambayan dalilin da yasa ya dade bai shigo ba sai suka tarar yana sume.

Asali: Legit.ng

Online view pixel