'A Soke EFCC,' Matasan Ibadan Suka Fada Wa FG, Sun Yi Babban Zanga-Zanga

'A Soke EFCC,' Matasan Ibadan Suka Fada Wa FG, Sun Yi Babban Zanga-Zanga

  • An bukaci gwamnatin tarayya gwamnatin tarayyar Najeriya ta soke hukumar yaki da rashawa ta EFCC
  • Wasu matasa ne a garin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo suka yi kira ga gwamnati ta soke hukumar
  • A cewar matasan, jami'an na hukumar EFCC sun dade suna kama su ba bisa ka'ida ba kan zarginsu da yin damfara ta intanet

Ibadan - Wasu matasa a ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba sun yi kira ga gwamnati ta soke Hukumar yaki da rashawa ta EFCC.

Matasan, ranar Alhamis 7 ga watan Oktoba, sun yi tattaki zuwa sakatariyar gwamnatin jihar Oyo da ke Agodi a Ibadan.

Zanga-zanga
'A Soke EFCC,' Matasan Ibadan Suka Fada Wa FG, Sun Yi Babban Zanga-Zanga. Hoto: The Nation.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Tsaron Ministan Abuja Hari

Sun nuna rashin jin dadinsu kan ayyukan da EFCC ke yi a jihar, musamman ga matasa a Ibadan.

Da suka isa sakatariyar, matasan sun yi ikirarin cewa jami'an na hukumar yaki da rashawa sun dade suna zin dalin matasa a garin.

Kuma, sun rika rera wakokin hadin kai, dauke da takardu masu rubutu daban-daban a jerin gwanon motocci kimanin 20 suka rika janyo cinkoson ababen hawa a Bodija Parliament Road, Total Garden Roads da wasu hanyoyin.

The Nation ta rahoto cewa zanga-zangan matasan ya janyo wa baki da masu ababen hawa a birnin bata lokaci na awanni.

Da ya ke magana kan lamarin, daya cikin masu zanga-zangan, wanda ya ce sunansa Samuel ya ce suna kokawa ne kan kama su barkatai ba bisa ka'ida ba da EFCC ke yi.

Samuel ya yi ikirarin cewa sau da yawa jami'an hukumar sun sha kama matasan Ibadan suna zarginsu da aikata damfara ko kasancewa 'Yahoo Boys'.

Kara karanta wannan

Rudani: Bayan dogon nazari, kotu ta wanke Magu daga zargin almundahana

Kalamansa:

"Ba cewa muke kar su yi aikinsu ba amma su yi shi bisa tsarin doka. Sun tare mutane, su rika bincika wayoyinsu. Wane irin abu ne wannan?".

Hukumar EFCC Ta Magantu Kan Dalilinta Na Kai Samame Gidan Alkali Mbaba Da Ke Kano

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi watsi da rahotannin cewa jami’anta sun kai mamaya gidan alkalin kotun daukaka kara, reshen Kano, Justis Ita Mbaba.

EFCC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 21 ya watan Satumba ta hannun kakakinta, Wilson Uwujaren.

Asali: Legit.ng

Online view pixel