Yadda Matar Malamin Addini, Yaransa 2 Da Kanne Mata 2 Suka Yi Mutuwar Ban Mamaki

Yadda Matar Malamin Addini, Yaransa 2 Da Kanne Mata 2 Suka Yi Mutuwar Ban Mamaki

  • Al'ummar Amutenyi, da ke Obollo-Afor, karamar hukumar Udenu ta jihar Enugu sun tashi da wani mummunan al'amari
  • Matar wani malamin addini, yaransu biyu da kuma kannensu mata biyu sun yi mutuwar ban mamaki
  • Mamatan biyar sun kwanta bacci a daren ranar Juma'a amma kuma basu sake farkawa ba

Enugu: An tsinci matar wani malamin addini mai suna Adolphus Odo kwance a mace tare da yaranta biyu da kuma kannenta biyu a Amutenyi, da ke Obollo-Afor, karamar hukumar Udenu ta jihar Enugu a ranar Asabar.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa karar kararrawar agogo ce ta ankarar da makwabta inda suka fasa kofar kawai sai suka tsinci mutanen su biyar kwance babu rai a jikinsu.

Jihar Enugu
Yadda Matar Malamin Addini, Yaransa 2 Da Kanne Mata 2 Suka Yi Mutuwar Ban Mamaki Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Da yake tabbatar da lamarin, shugaban karamar hukumar, Solomon Onah, ya ce labarin ya jefa yankin karamar hukumar cikin alhini.

Kara karanta wannan

Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

Onah ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Mun ga gawarwakinsu a safiyar yau Asabar. Bamu riga mun san abun da ya haddasa mutuwar tasu ba amma dai an kwashi mamatan zuwa Enugu domin yi masu gwaji.
“Da muka isa gidansu, mun ga murhun hura gawayi a cikin dakin da suka mutu, koda dai babu wuta a kinsa, ba za mu zargi hayakin injin janareto ba saboda basu yi amfani da shi ba a daren jiya. Bamu riga mun gano abun da ya haddasa lamarin ba har zai mun samu sakamakon gwajin gawar.”

Malamin addinin, Odo, yana cikin kaduwa da ba zai iya cewa komai ba a yanzu.

Kakakin yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, rahoton Premium Times.

Ya ce an kai rahoton lamarin ofishin yan sanda da misalin karfe 9:25 na safiyar Asabar. Lamarin ya afku ne Amutenyi, Obollo-Afor, karamar hukumar Udenu.

Kara karanta wannan

Hankula Sun Tashi Yayin Da Aka Nemi Mutum 30 Aka Rasa Sakamakon Kifewar Kwale-Kwale A Wata Jihar Najeriya

Mista Ndukwe ya ce binciken farko ya nuna cewa mamatan sun kwanta bacci da dare amma kuma basu tashi ba washegari.

Kakakin yan sandan yace jami’an su sun garzaya yakin bayan amsa kira kawai sai suka gano mutanen kwance cikin wani hali a dakuna biyu mabanbanta da ke gidan.

Kwamishinan yan sandan jihar, Ahmed Ammani, ya yi umurnin bincike cikin lamarin.

Gaskiya Ta Fito: 'Yadda Muka Shawo Kan Yan Ta'adda Suka Sako Ragowar Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja'

A wani labari na daban, sakataren kwamitin mutum bakwai na shugaban ma’aikatan tsaro, Farfesa Usman Yusuf, ya magantu kan al’amarin sakin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Farfesa Yusuf yace sun shafe tsawon watanni shida suna aiki ta karkashin kasa domin tabbatar da ganin cewa an saki fasinjojin ba tare da an biya fansa ba, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

Hakan ya kasance ne yayin da yace kwamitinsu bai karfafa biyan yan ta’addan kudin fansa ba.

Kara karanta wannan

Yadda Direban Babban Mota Da Wani Suka Sumar Da Jami'in Kula Da Cinkoson Ababen Hawa A Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel