Hotunan Yadda Wani Bakano Ya Kera Keke Napep Tun Daga Tushe

Hotunan Yadda Wani Bakano Ya Kera Keke Napep Tun Daga Tushe

  • Wani Bakano ya ba da mamaki yayin da ya nuna keke napep din da ya kera daga tushe kuma yake amfani da ita
  • An ga hotunan Faisal a lokacin da yake aikin kiran da kuma lokacin da ya kammala har ta kai ga yana iya tuka ta
  • Jama'a a kafar sada zumunta sun sha mamaki, sun roki gwamnati ta taimakawa matashi irin wannan

Kano - Wasu hotuna da jarida Punch ta yada a kafar Twitter sun nuna wani matashi dan jihar Kano da ya kera keke napep tun daga tushe.

An ga hoton matashin mai suna Faisal a jikin keke napep din aka ce ya kera.

Bakano ya kera keke napep daga tushe
Hotunan Yadda Wani Bakano Ya Kera Keke Napep Tun Daga Tushe | Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Mutane da dama a kafar sada zumunta sun yi martani bayan ganin hazikin matashin dan Najeriya ya kera daya daga abubuwan sufuri da ake amfani dashi.

Ba sabon abu bane samun hazikan 'yan Najeriya dake kokarin kawo mafita da baje-kolin kwarewarsu a fannin kimiyya a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli hotunan:

Martanin jama'a

@Herneholar yace:

"Wannan abu ya yi kyau."

@geezoopita yace:

"Ka yi kokari Faisal. Muna bukatar irin ka da da yawa."

@Lokosoeru yace:

"A nan ya kamata Gandollar yake zuba kudadensa a matsayin hannun jari."

@frequency100 yace:

"Idan har wani zai iya kirkirar wannan daga tushe, meye yasa #FG ke shigo da irinsa kuma ake siyarwa da tsadan ban dariya? Sama nda #800,000.
"Wannan abu zai iya kawo wa Najeriya alheri idan har 'yan siyasa basu yi babakerensa ba!."

@OluwatayoOluwa3 yace:

"Muna da hazikan 'yan Najeriya, wannan abu ne mai kyau idan gwamnatu za ta tallafi wannan mutumin za mu gogayya da kowace kasa a duniya."

Kyakkyawar Mata ’Yar Najeriya Ta Fito Fili, Ta Bayyana Soyayyar da Takewa Mijinta Makaho

A wani labarin, Mariam, wata kyakkyawar mata 'yar Najeriya ta yi kaurin suna a shafin intanet yayin da ya ba da labarin aurenta.

A wani bidiyon hira da ita, ta ce tana auren wani makaho ne mai suna Toyin Bello wanda ke sana'ar tallan man wanki, ya rasa idanunsa ne shekaru bakwai da suka gabata.

Da aka tambayi me yasa ta auri Bello, ta ce ta kamu da kaunarsa ne, don haka ta toshe kunne ga tssgumin jama'a ta yi wuf da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel