Kyakkyawar Mata ’Yar Najeriya Ta Fito Fili, Ta Bayyana Soyayyar da Takewa Mijinta Makaho

Kyakkyawar Mata ’Yar Najeriya Ta Fito Fili, Ta Bayyana Soyayyar da Takewa Mijinta Makaho

  • Wata kyakkayawar mata 'yar Najeriya mai suna Mariam da ta auri makaho ta bayyana labarin soyayyarsu
  • A wata tattaunawa da aka yi da ita, an tambayi matar ko da saninta ta zabi aure tare da zama da makohon
  • Cikin farin ciki, ta bayyana cewa, bata taba danasanin aurensa ba wai don shi makaho ne, tana matukar kaunarsa

Mariam, wata kyakkyawar mata 'yar Najeriya ta yi kaurin suna a shafin intanet yayin da ya ba da labarin aurenta.

A wani bidiyon hira da ita, ta ce tana auren wani makaho ne mai suna Toyin Bello wanda ke sana'ar tallan man wanki, ya rasa idanunsa ne shekaru bakwai da suka gabata.

Kyakkyawar matar da ta auri makaho
Wata Kyakkyawar Mata ’Yar Najeriya Ta Fito Fili, Ta Bayyana Soyayyar da Takewa Mijinta Makaho | Hoto: BBC Pidgin
Asali: Instagram

Da aka tambayi me yasa ta auri Bello, ta ce ta kamu da kaunarsa ne, don haka ta toshe kunne ga tssgumin jama'a ta yi wuf da shi.

Kara karanta wannan

Range Rover Nake So: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Motar Wasan Yara Yayin da Ta Dame Shi Ya Siya Mata Mota

Bello ya shaidawa BBC Pidgin cewa, dan uwansa ne ya kawo masa Mariam, ya shaida masa cewa tana matukar son ta aure shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello ya ce ya sha matukar mamakin yadda matar ta dage za ta aure shi. Ya tambaye tra dalili, tace kawai tana kaunarsa ne.

A bangarenta, Mariam ta bayyana yadda jama'a ke yi mata ba'a saboda ta auri makaho, musamman kawayenta duk da cewa ita dai lafiyarta lau kuma 'yar kwalisa.

Duk da haka, ta yanke shawarin nan mai tsauri, ta auri makaho kana ta ci gaba da rayuwarta cikin farin ciki.

Hakazalika, ta ce sam bata taba yin dana-sani ba, domin kaunar da take masa ba iyaka.

Martanin jama'a

Ustakay yace:

"Na jinjinawa wannan mutumin bisa neman abin da zai yi ba wai ya karade gari yana bara ba."

Kara karanta wannan

Matar Aure Dake Zama Gida Daya da Mijinta da Saurayinta Tace Duniya Tayi mata Dadi

__kach22 yace:

"Ta auri ruhinsa ne ba wai jikinsa ba. Soyayya ta fi siffa kari."

Chyoma.oma tace:

"Wow! Allah ya yi musu albarka. Mutumin ma musamman, dogo kuma kyakkyawa."

1406shopifyglobal_ltd yace:

"Kyakkyawan mutum ne! Allah ya yi musu albarka dukansu ya kuma turo mai taimaka musu."

Samuyiiguokundia yace:

"Tabbas soyayya aba ce da mutum ke ji haka kawai, ba wai ido ne ke gano ta ba. Allah madaukaki ya ci gaba sanya musu albarka a zamantakewarsu da komai"

Ifeoluwa.abimbola yace:

"Soyayya ta fi karfin duk wani tunaninmu. Da yardar Allah wata rana zai sake gani (Amin)."

Bidiyon Yaro Makanike Na Zuba Turanci Ya Ba Jama’a Mamaki

A wani labarin, dandazon mutane a shafin TikTok sun kamu da kaunar wani yaro mai suna Mubarak saboda irin kwazon da yake dashi.

Hakan ya fara ne daga wani bidiyon da @ayofeliberato ya yada na lokacin da Mubarak ke karanta wata muhawara da ta dauki hankali ya yadu a intanet.

Kara karanta wannan

Auren Cin Amana Tsohuwar Matar Adam Zango Tayi, Jaruma Safna Ta Fasa kwai

Kwarewarsa a yaren turanci ta ba jama'a mamaki, wannan yasa suka ce ya yi matukar burge su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel