Shugaban Majalisar Najeriya, Ahmad Lawan, Ya Bayyana Su Wanene Manyan Makiyan Kasar

Shugaban Majalisar Najeriya, Ahmad Lawan, Ya Bayyana Su Wanene Manyan Makiyan Kasar

  • Dr Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya ya ce barayin danyen man fetur sune manyan makiyan kasar
  • Lawan ya bayyana hakan ne a zauren majalisar tarayya a ranar Juma'a yayin da Shugaba Buhari ke gabatar da kasafin kudin 2023
  • Sanata Lawan ya ce barayin danyen man suna janyo wa kasar asarar kudi kimanin kashi 35 cikin 100 na kudin da ya kamata a samu daga man

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan ya bayyana barayin danyen man fetur a matsayin manyan makiyan Najeriya.

Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 a zauren majalisar da ke Abuja a ranar Juma'a.

Danyen Mai
Barayin danyen man fetur ne manyan makiyan Najeriya, Lawan. Photo: Akintunde Akinleye
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kasafin Kudi: Buhari Ya Fadawa Majalisa Ba Zai Cigaba da Biyan Tallafin Fetur a 2023 ba

Daily Trust ta rahoto Lawan ya ce Najeriya tana rasa kimanin ganga 700,000 zuwa 900,000 na danyen man fetur a duk rana, wanda ya kai kashi 35 cikin 100 na asarar kudin mai.

Ya ce:

"Satar danyen mai da ake yi a Najeriya ya kai mummunan mataki. Yanzu Najeriya na rasa kimanin ganga 700,000 zuwa 900,000 na danyen man fetur a duk rana, wanda ya kai kashi 35 cikin 100 na asarar kudin mai.
"Barayin danyen man fetur ne manyan makiyan wannan kasar kuma sun ayyana yin yaki da kasar. Don haka, dole a dauki tsatsauran mataki don dakile satar da barayin ke yi."

Lawan ya yi wa Buhari godiya saboda gabatar da kasafin kan lokaci

Lawan ya mika godiya ta Shugaba Muhammadu Buhari saboda gabatar da kasafin kudin a kan lokaci, wanda ya ce zai ba wa majalisar isashen lokacin duba wa da kuma amincewa da shi.

Kara karanta wannan

Buhari zai Gabatar da Kasafin Kudi a Yau, Tsaro ya Tsananta a Farfajiyar Majalisa

Ya bada tabbacin cewa mambobin majalisar za su mayar da hankali su tabbatar an amince da kasafin kufin kafin karshen shekara kamar yadda aka yi na baya.

Ya bukaci cewa kasafin na 2023 ya mayar da hankali wurin kammala ayyukan da ake yi yanzu, musamman manya wadanda za su zama na tarihi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel