Yajin-aiki: Kotu Ta Fadawa ASUU da Gwamnati Yadda Za Su Shawo Kan Sabaninsu

Yajin-aiki: Kotu Ta Fadawa ASUU da Gwamnati Yadda Za Su Shawo Kan Sabaninsu

  • Kungiyar malaman jami’a watau ASUU sun daukaka kararsu da gwamnatin tarayya a babban kotu
  • Da aka zauna a kotun daukaka kara, Georgewill Abraham ya bukaci bangarorin suyi sulhu da junansu
  • Alkali yana sa rai nan da gobe a ji an sasanta tsakanin Gwamnati da kungiyar ASUU, a jefar da karar

Abuja - Babban kotun daukaka kara da ke zama a birnin tarayya na Abuja ta saurari karar da kungiyar ASUU ta shigar a kan gwamnatin tarayya.

Rahoton da ya fito daga gidan talabijin na Channeles TV yace Alkali fadawa kungiyar malaman jami’a da gwamnatin tarayya su sasanta wajen kotu.

Babban lauyan da ya tsayawa kungiyar ASUU, Femi Falana (SAN) da James Igwe (SAN) mai kare gwamnatin tarayya sun halarci zaman da aka yi dazu.

Mai shari’a Georgewill Abraham ya bada shawara ga bangarorin biyu su zauna da junansu domin su cin ma matsaya a kan abin da zai ceci ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

ASUU Bata Da Wasu Dalilai Masu Kwari Na Ci Gaba Da Yajin Aiki - Buhari

The Cable ta rahoto Alkalin yana fadawa lauyoyin da suka tsayawa ASUU da gwamnati su zauna a kan tebur nan da awa 24 domin a samu maslaha.

Komai da lokacinsa - Alkali

“Akwai lokacin komai; akwai lokacin fada, akwai na zaman lafiya.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

University of Jos
Jami'ar Uni Jos Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“A matsayinku na manya a gidan shari’a, muna so ku biyu ku zauna tun da ku manyan lauyoyi ne, ku bada shawarar a samu maslaha a wannan rikici.”
“Kai muna so a dawo zaman kotu ranar Alhamis dinnan da labari mai dadi cewa an dinke barakar, idan aka yi haka, duk ‘Yan Najeriya za su gode maku.
“Saboda haka ku yi magana da wadanda ku ke karewa, su duba kishin kasa da halin yaranmu. Idan kun bar nan, ku je ku zauna domin shawo kan batun.”

Punch ta rahoto James Igwe da Femi Falana sun amince za su bi shawarar Alkali Abraham, za suyi kira ga bangarorin malamai da gwamnati su koma tebur.

Kara karanta wannan

Idan Nayi Nasara Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arziki Kasar, Kwankwaso Ya Yi Alkawari

Hushpuppi zai je kurkuku?

Mun ji labari Ramon Abbas watau ‘Hushpuppi’ ya nemi a yanke masa hukunci mara tsauri sosai saboda ya ba jami’an tsaro hadin-kai a kasar Amurka.

Amma Lauyoyin Gwamnatin kasar ta Amurka da suka shigar da kara sun ce akwai bukatar Hushpuppi ya yi shekaru 11 yana tsare a makargama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel