Boyayyun Hadimai 11 da ke Cikin Aso Rock Villa da Aikin da Kowa Yake Yi wa Buhari

Boyayyun Hadimai 11 da ke Cikin Aso Rock Villa da Aikin da Kowa Yake Yi wa Buhari

  • Akwai wasu daga cikin Hadiman shugaban kasa da mutanen Najeriya da-dama ba su san da zamansu ba
  • Masu taimakawa Mai girma Muhammadu Buhari sun hada da Likitoci har zuwa masu kula da cikin dakinsa
  • Daga cikin wadanda suke aiki a fadar shugaban Najeriyan akwai Masu daukarsa hotuna a duk inda ya shiga

Mun tattaro jerin Hadiman shugaban kasar kamar yadda aka fitar da sunayensu a lokacin da aka sake nada su a Mayun 2019.

1. Mohammed Sarki Abba

Babban Mai taimakawa shugaban kasa na musamman a kan harkokin gida da taron jama’a.

2. Ya’u Shehu Darazo

Babban Mai taimakawa shugaban kasa na musamman a kan ayyuka na musamman.

3. Dr. Suhayb Sanusi Rafindadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Jam’iyyar PDP Za Ta Kira Taron Gaggawa Domin Ceton Takarar Atiku Daga Watsewa

Likitan da ke kula da lafiyar Mai girma shugaban kasa.

4. Amb. Lawal A. Kazaure

Mai kula da tsare-tsaren fadar Shugaban kasa

5. Sabiu Yusuf (Tunde)

Mai taimakawa na musamman (a ofishin shugaban kasa).

Mai taimakawa Buhari
Sabiu Yusuf Mai taimakawa Shugaban kasa Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

6. Saley Yuguda

Mai taimakawa na musamman (a wajen kula da gida).

7. Ahmed Muhammed Mayo

Mai taimakawa na musamman (a wajen tattalin kudi da gudanarwa).

8. Mohammed Hamisu Sani

Mai taimakawa na musamman (a wajen ayyuka na musamman).

9. Friday Bethel

Mai taimakawa Shugaban kasa (Ayyukan yau da gobe).

10. Sunday Aghaeze

Mai taimakawa wajen daukar hoto a fadar Shugaban kasa

11. Bayo Omoboriowo

Mai taimakawa wajen daukar hoton Mai girma Shugaban kasa

Sauran masu aiki a Aso Villa

Wannan jeri bai kunshi masu magana da yawun bakin Muhammadu Buhari da sauran wadanda suke taimaka masa wajen harkokin ofishinsa ba.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasan gaba daya shi ne Farfesa Ibrahim Gambari wanda ya canji Malam Abba Kyari bayan rasuwarsa a 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel