Mai Iyali: Hotunan Malamin Makaranta Ya Haifa ‘Da na 19, Ya auro Mata ta 4

Mai Iyali: Hotunan Malamin Makaranta Ya Haifa ‘Da na 19, Ya auro Mata ta 4

  • Malam Muhammad Sulaiman, malamin kwalejin ilimi mai tarin iyali da yara uku ya bayyana cewa ya samu karuwa
  • Mai tarin iyalin ya sanar da cewa, a ranar daya da ya aurar da diyarsa ne ya auro matarsa ta hudu duk a ranar
  • Mahaifin yaran 18 a baya ya sanar da cewa yanzu ya zama mai yara 19 da mata hudu cif inda ya rufe kofa gaba daya

Malamin makarantan nan mai tarin iyalai da mata uku mai suna Malam Sulaiman Muhammad, ya haifa ‘da na 19 inda ya bayyana hotunan a shafinsa na Facebook.

Kamar yadda mahaifin yara 19 din mai mata uku ya bayyana, ya sanar da cewa ya aura mata ta hudu inda ya rufe kofa da ita.

Mai Iyali
Mai Iyali: Hotunan Malamin Makaranta Ya Haifa ‘Da na 19, Ya auro Mata ta 4. Hoto daga Sulaiman Mohammed
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Wani Jagoran Jam’iyya Ya Fadi Ainihin Silar Zuwan Bola Tinubu Kasar Waje

Har ila yau, Muhammad Sulaiman ya bayyana yadda ya aurar da diyarsa daya inda a rana daya ya auro mata ta hudu tare da samun karuwar yaro.

Magidanci yayi shagalin sallarsa da matansa 3 da 'ya'ya 19, hotunansu sun janyo cece-kuce

A wani labari na daban, wani 'dan Najeriya yayi shagalin bikin sallah babba inda har ya bayyana hotunansa tare da matansa uku reras da 'ya'yansa 19.

Bawan Allah mai suna Baba Lawal, ya wallafa kyawawan hotunan ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yulin 2022 a shafinsa na Facebook.

A hotunan sun yi ankon kaya kalar kasa mai duhu yayin da matan suka saka hijabai kalar kayan mijinsu da 'ya'yansu sannan suka sanya niqabai a fuskokinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel