Magidanci yayi shagalin sallarsa da matansa 3 da 'ya'ya 19, hotunansu sun janyo cece-kuce

Magidanci yayi shagalin sallarsa da matansa 3 da 'ya'ya 19, hotunansu sun janyo cece-kuce

  • Wani magidanci ya gigita kafafen sada zumuntar zamani da hotunanshi tare da matansa uku reras da jerin 'ya'yansu
  • Ba wannan ya kara janyo cece-kuce ba, ganin shi da yara 19 ya matukar birge jama'a da kuma yadda suka zuba ankon kaya launi daya
  • An ga magidanci Baba Lawal tare da matansa dake sanye da niqabai a fuskokinsu yayin da yaransu 19 suke zagaye dasu abun sha'awa

Wani 'dan Najeriya yayi shagalin bikin sallah babba inda har ya bayyana hotunansa tare da matansa uku reras da 'ya'yansa 19.

Bawan Allah mai suna Baba Lawal, ya wallafa kyawawan hotunan ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yulin 2022 a shafinsa na Facebook.

Baba Lawal da iyalansa
Magidanci yayi shagalin sallarsa da matansa 3 da 'ya'ya 19, hotunansu sun janyo cece-kuce. Hoto daga Baba Lawal
Asali: Facebook

A hotunan sun yi ankon kaya kalar kasa mai duhu yayin da matan suka saka hijabai kalar kayan mijinsu da 'ya'yansu sannan suka sanya niqabai a fuskokinsu.

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan barka da sallah daga gidan ango Lilin Baba da amaryarsa Ummi Rahab

Lawal, wanda 'dan asalin jihar Kwara ne, yana koyarwa a kwalejin ilimi ta Umar Bn Khattab dake Kaduna kuma shine sakataren hukumar Hisbah na jihar Kaduna kamar yadda bayanansa na shafinsa a Facebook suka nuna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jama'a sun yi martani kan hotunan Lawal da iyalansa

A yayin martani kan labarin, Joseph Ameh yace: "Wannan ai matsala ce, kayyade haihuwa yana da matukar amfani idan muna son ganin daidai a kasar nan! tarbiya ta fi karfin ciyarwa, akwai abubuwa da yawa da ake yi."
Maikudi Aliyu yace: "Wannan yayi kyau! Muna fatan muma mu samu irn wannan albarkar. Mahaifina 'ya'ya 21 gare shi, dukkansu suna da digiri! Kuma kowanne daga ciknmu yana rayuwa mai kyau. Alhamdulillah. Zai cik shekaru 82 a wannan watan Satumban. Godiya ta tabbata ga Allah."
Gonet Nensok cewa yayi: "Meye amfanin hoton nan da mata duk fuskoki a rufe? Sannan kuma komai ba daidai yake ba da wannan yawan ahihuwar, kawai yawansu ne amfanin."

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyo: Dandazon jama'a sun fito nuna wa Buhari kauna yayin da yake takawa zuwa gida daga idi

Queen Esom tace: "Bani da matsala matukar yana ciyar dasu kuma yana kula da su yadda ya dace."
Marshal Sampson tsokaci yayi da: "Amma zai iya auren dukkan matan uku ba tare da wadannan buyagin 'ya'yan ba. Kowacce mata za ta iya haifar yara uku kuma a zauna cikin farin ciki. Me zai sa a dorawa kai dawainiya?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel