Wani Jagoran Jam’iyya Ya Fadi Ainihin Silar Zuwan Bola Tinubu Kasar Waje

Wani Jagoran Jam’iyya Ya Fadi Ainihin Silar Zuwan Bola Tinubu Kasar Waje

  • Ba komai ya sa Asiwaju Bola Tinubu ya tafi kasar Birtaniya ba, illa iyaka ya samu damar da zai sarara
  • Wannan shi ne hujjar da Ayo Oyalowo ya bada yayin da aka nemi jin ina ‘dan takaran APC ya shiga
  • Oyalowo yace an lura Tinubu bai samun isasshen hutun da ya kamata, saboda haka ya tafi kasar waje

Abuja - A lokacin da aka fara yakin neman zabe, sai ga shi Asiwaju Bola Tinubu mai neman shugabancin Najeriya a inuwar APC mai mulki ya bar kasar.

Da aka zanta da Ayo Oyalowo a gidan talabijin na Arise TV, ‘dan siyasar ya bayyana abin da ya sa ‘dan takara na su ya tafi Ingila, ya kuma ce lafiyansa lau.

Kara karanta wannan

Yadda Na Ga Lafiyar Tinubu Kafin Ya Bar Najeriya, Ya Tafi Birtaniya Inji Jigon APC

Ayo Oyalowo ya shaida cewa Bola Tinubu ya tafi birnin Landan ne da nufin ya huta domin a nan Najeriya, jama’a ba za su kyale shi ya samu damar hutu ba.

Ba za su bar shi ya samu hutu ba

“Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana London. Ba zai iya hutawa a Legas ba, ba za su bar shi ya huta.
“Yana yawan zuwa Abuja, a nan ma ba za su kyale shi yah uta ba. Wannan mutumi yana aikin awa 20 a rana.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Saboda haka sai mutane masu hankali suka ga ya kamata ya samu hutu tun da lokacin kamfe ya karaso."

- Ayo Oyalowo

Bola Tinubu
Bola Tinubu mai neman mulki a 2023 Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Ba a ga Tinubu a taro ba

A yau Daily Trust ta rahoto Oyalowo yana cewa an gayyaci ‘dan takaran wajen yarjejeniyar zaman lafiya ne bayan ya bar Najeriya, ya tafi ketare

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu ya ce zai ba 'yan Najeriya mamaki, zai sauya makomar Najeriya

Jagoran na APC yace a sa'ilin da goron gayyatar ta zo, shi kan shi Kashim Shettima ya na Maiduguri, amma dolensa ya kama hanya ya dawo Abuja a lokacin.

“Goron gayyatar yarjejeniyar zaman lafiya ya zo ne bayan Tinubu ya fice daga kasar nan.
Shi kan shi abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima bai gari a lokacin, sai da ya bar abin da yake yi a Maiduguri.”

Kamar yadda This Day ta rahoto, Oyalowa wanda yana cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben APC ya karyata rade-radin cewa ‘dan takararsu ya na asibiti.

Tinubu garau yake

A baya kun ji labari mutane suna yada labari mara tushe cewa ‘dan takaran shugaban kasar yana kwance babu lafiya, hakan ta sa ya tafi kasar Birtaniya.

Wani a jigo a tafiyar APC ya fadi halin da ya samu Bola Tinubu ana daf da zai tafi ketare, ya musanya jita-jitar da ke yawo cewa 'dan takaran yana jinya ne.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarki Sanusi Ya Ragargaji Gwamnatin APC a gaban Majalisar Dinkin Duniya

Asali: Legit.ng

Online view pixel