Buhari zai karrama Abba Kyari, Tunde, Okonjo-Iweala da Wasu 437 da Lambar Girma

Buhari zai karrama Abba Kyari, Tunde, Okonjo-Iweala da Wasu 437 da Lambar Girma

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya sa sunan Abba Kyari a mutane 437 da za a karrama a bana
  • Kwanan nan Gwamnatin tarayya za ta bada lambar girmamawa na shekarar 2022 ga fitattun mutane
  • Za a raba lambar GCON, OFR, OON, MFR, MON, da kuma FRM ga irinsu Dr. Ngozi Okonjo-Iweala

Abuja - Wani rahoto da Premium Times ta fitar a ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba 2022, ya nuna Ngozi Okonjo-Iweala tana cikin wadanda za a karrama.

Za a ba shugabar kungiyar WTO da sauran wadanda aka zaba wannan lambar yabo ne a ranar 11 ga watan Oktoba. Za ayi bikin a fadar shugaban Najeriya.

Mutane har biyar za a ba lambar GCON, sannan za a ba wasu mutum 54 lambar girma na CFR. Sannan akwai mutane 67 da za su karbi CON a shekarar nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Karrama Buratai Da Babban Lambar Yabo Na Kasa

Rahoton yace an ware mutane 64 da za su karbi OFR, sai 101 da za a karrama da OON. Har ila yau, za a raba MFR, MON da FRM ga fitattun mutane kusan 140.

Marigayi Abba Kyari yana sahun wadanda za a ba CFR. Shugaban bankin AfDB, Akinwumi Adesina da Okonjo-Iweala za su samu OON da kuma GCON.

Lambar girma
Okonjo-Iweala, Burna Boy. Amina J. Mohammed za su samu lambobin yabo Hoto: Legit
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda aka yi rabon lambobin

GCON

Wannan babbar lambar girma za ta je ga Sanata Ahmad Lawan; Kayode Ariwoola, Tanko Muhammad da Amina J. Mohammed da ke UN.

CFR

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila; Janar Lucky Irabor; Rt. Hon. Yakubu Dogara, Mai shari’a Monica Mensem da IGP Usman Alkali Tukur Buratai za a ba CFR.

Haka zalika Sarakunan kasar Zazzau, Lafia, Ahmad Nuhu Bamalli, Sidi Bage, da Tor Tiv, Farfesa James Ayatse.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen 'Yan Takara 10 na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya

OFR

Ignatius Kaigama, shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kolo Kyari, Mai martaba Nasiru Bayero da fitaccen lauyan nan, Muiz Banire za su samu lambar OFR.

OON

Daily Trust ta kawo sunan Hon. Alhassan Doguwa, Muktar Betara, Ndudi Elumelu da Nkiruka Onyejeocha. Sai Sunday Echono, shugaban NBA, Yakubu Maikyau, Sarki Abba, da Sabiu (Tunde) Yusuf

MFR

A sahun nan akwai Sanusi Lemu, Marigayi Joseph Egunike Haliru Nababa da Burna Boy.

MON

A wannan sahu akwai mawaka da makada irinsu 2Face Idibia, Teni, Shehu Othman da Abubakar Maikano.

...Da sauransu

Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede da wasu mutane 67 za su samu CON.

Sababbin SAN a Najeriya

An ji labari Kwamitin LPPC na malaman shari’a ya amince da karin matsayin wasu Lauyoyi zuwa matsayin SAN ta bakin Sakatariyar LPPC, Hajo Bello.

Da farko sunayen lauyoyi 129 aka fitar, daga cikinsu ne aka zabi 62 da suka yi fice a wajen aiki. Duk wanda ya zama SAN, ya yi zarra a bangaren shari'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel