Jerin Sunayen Farfesoshi 5 da Suka Mutu a Lokacin Yajin ASUU a Jami’ar Calabar

Jerin Sunayen Farfesoshi 5 da Suka Mutu a Lokacin Yajin ASUU a Jami’ar Calabar

  • Mambobin kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) reshen jami'ar Calabar a jihar Kuros Riba ta kirga yawan mambobinta da ta rasa a lokacin yajin aiki
  • Dr John Edor, shugaban ASUU reshen jami'ar Calabar ya ce akalla lakcarori 10 aka yi rashi tun fara yajin aikin zuwa yanzu
  • Sai dai, Dr Edor ya ce kungiyar za ta ci gaba da jure duk wata wahala a wannan fafutuka da ake na martaba aikin karantarwa a Najeriya

Calabar, jihar Kuros Riba - Akalla mambobin kungiyar malaman jami'a ta ASUU 10 ne a jami'ar Calabar a jihar Kuros Riba suka riga mu gidan gaskiya a lokacin wannan yajin aikin da kungiyar ke yi tun watan Fabarairu.

Dr John Edor, shugaban ASUU reshen jami'ar Calabar ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar a jiya Laraba 28 ga watan Satumba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Allah Ya Yiwa Sarkin Lokoja, Dr Muhammadu Maikarfi, Rasuwa

Lakcarori 10 sun mutu a jami'a a lokacin yajin aiki ASUU
Jerin Sunayen Farfesoshi 5 da Suka Mutu a Lokacin Yajin ASUU a Jami’ar Calabar | Hoto: University of Calabar
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana cewa, daga wadanda aka rasan akwai farfesoshi biyar, sabanin labarin da aka yada cewa lakcarori lakcarori 21 ne aka rasa a jami'ar, rahoton Daily Post.

Dr Edor ya bayyana sunayen farfesoshi 5 da suka mutu:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

  1. Professor Gabriel U. Ntamu
  2. Professor Judith Otu
  3. Professor Udosen
  4. Professor Kate Agbor
  5. Professor Obia

Yajin ASUU babu gudu babu ja da baya, inji Dr Edor

A cewarsa, duk da irin wahala da kuma rasa mambobi da kungiyar ta yi, tabbas babu abin da zai girgiza su a neman hakkinsu da suke a hannun gwamnati.

"Duk da halin ko in kula da tsoratarwa daga gwamnatin tarayya, ba za mu daga kafa ba game da bukatunmu.
"Duk da yadda gwamnati ta ki sauraran kokenmu tare da samar da mafita mai daurewa, za mu ci gaba da jure rashin da muke samu."

Kara karanta wannan

Kamfen zaben 2023: Tinubu ya fadi sassan da zai tafi yawon kamfen a Najeriya

Gwamnatin Buhari Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Janye Umarnin da Ta Bayar Na Bude Jami’o’i

A wani labarin, gwamnatin tarayya, ta hannun hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC) a yammacin yau Litinin 26 ga watan Satumba ta janye umarnin da ya ba shuganannin jami'o'i na su koma bakin aiki, Vanguard ta ruwaito.

A wani rahoton da muka samo da sanyin safiyar yau, an wata wasika mai lamba NUC/ES/138/Vol.64/135 da NUC ta fitar ta umarci shugabannin jami'o'in gwamnati a Najeriya da su bude makarantu tare da kiran dalibai su dawo makaranta.

Sai dai, a wata sabuwar wasika mai lamba NUC/ES/138/Vol.64/136, hukumar ta NUC ta janye batun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel