Fasaha Tsantsa: Yadda Wani Dan Najeriya Ya Mayar Da Kwantena Ya Zama Hadadden Ofis, Bidiyon Ya Yadu

Fasaha Tsantsa: Yadda Wani Dan Najeriya Ya Mayar Da Kwantena Ya Zama Hadadden Ofis, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani matashi ya sha ruwan yabo a TikTok saboda ya mayar da tsohon kwantena ya zama hadadden ofis
  • A bidiyon wanda ya wallafa a dandalin, mutumin ya nuno sabbin ofis da yasa mutane da dama suka nuna sha’awarsu na mallakar daya
  • Bidiyon ya tara martani da dama daga masu amfani da TikTok, wasu sun ce zai iya zama wani hanya na yin gini

Wani dan Najeriya ya wallafa wani hadadden bidiyo a TikTok yana mai nuna yadda ya mayar da kwantena suka zama ofis-ofis.

Ya nuno hadaddun ofis-ofis din a shafin TikTok mai suna @tinspaces kuma nan take ya yadu.

Kwantena
Fasaha Tsantsa: Yadda Wani Dan Najeriya Ya Mayar Da Kwantena Ya Zama Hadadden Ofis, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@tinspaces
Asali: UGC

Mabiyansa a dandalin sun kayatu da wannan fasaha tasa da kuma yadda aka mayar da kwantenan yayi kyau.

Amma da farko, duk wanda ya kalli kwantenan ba zai taba tunanin cewa zai iya amfani har ya zama ofis ba.

Kara karanta wannan

Mai kamar maza: Bidiyon budurwa mai tuka tirela ya girgiza intanet, jama'a sun shiga mamaki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, bayan ya yi aiki a kai sannan sanya shi a inda ya dace, ya ja hankalin mutane har suna son mallakar guda.

Kalli bidiyon a kasa:

Masu amfani da TikTok sun jinjinawa fasaharsa

Wani mai amfani da TikTok yace zai so ya mallaki irinsa guda daya amma yayi korafin tsadansa.

Wani mai amfani da dandalin yace ya kamata gwamnati ta ba mutumin kwangilar gina alkarya.

@Melusi Bhengu ya ce:

“Ina son wannan ido rufe amma kwantena na da tsada.”

@user2725642983873 ya ce:

"Yana da kyau amma sai zafin ciki yayi yawa mutum zai sani.”

Pemi Junior ya yi martani:

"Wai ido na yi mun ciwo ne?”

@rosekiss ta ce:

"Ina son wannan ta yaya zan same shi.”

@Anisah Shaik ta ce:

"Akwai bukatar gwamnati ta ba ka kwangilar gina alkaryarmu.”

Kara karanta wannan

Wasu Na Kishi: Matashi Ya Jinjinawa Matarsa Yayin da Take Girki Da Icce A Bidiyo

Aljannar Duniya: Bidiyon Katafaren Jirgin Sama Mai Dauke Da Dakunan Barci 2 Ya Yadu A Soshiyal Midiya

A wani labarin, tsarin cikin wani jirgin sama ya haifar da martani masu yawan gaske a Instagram bayan an dauki bidiyonsa tare da yada shi a dandalin na soshiyal midiya.

A cikin dan gajeren bidiyon mai numfashi, an hasko yadda aka kawata cikin jirgin gaba dayansa kuma hakan ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu.

Jirgin saman mai zaman kansa na dauke da manyan dukanan barci guda biyu da wasu wuraren zama da suka yi kama da kananan dakunan taro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel