Bidiyon Yadda Aka Fallasa Wata Budurwa Da Ke Bara Da Jinjirin Karya A Lagas

Bidiyon Yadda Aka Fallasa Wata Budurwa Da Ke Bara Da Jinjirin Karya A Lagas

  • An fallasa wata matashiyar budurwa da ke amfani da jinjirin bogi tana bara a jihar Lagas inda mutane suka yi martani
  • Wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno budurwar dauke da wani kunshi da ya yi kama da yaro yayin da take rokon kudi a wajen matafiya
  • Sai dai kuma wani matafiyi ya nace shi dai yana so ya ga abun da ta nannade a tsumman jego kafin ya bata wani abu

Lagas - Yan Najeriya sun kadu bayan ganin wani bidiyo na wata matashiyar budurwa da ke amfani da jaririn bogi tana bara da rokon kudi a jihar Lagas.

A cikin bidiyon, matashiyar budurwar ta nannade wani abu a tsumman jego sannan tana lallashinsa kamar yaro.

Budurwa
Bidiyon Yadda Aka Fallasa Wata Budurwa Da Ke Bara Da Jinjirin Karya A Lagas Hoto: @seunoloketuy.
Asali: Instagram

Amma mutumin da take rokon kudin a wajensa shima dan Lagas ne wanda ya san kan abun da suke yi.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Ya bayyana cewa lallai sai ya ga fuskar jinjirin kafin ya bashi wani abu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane da dama sun kadu lokacin da ta nuno fuskar abun da aka nannade, babu jinjiri sai mutum-mutumi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Yan Najeriya sun yi martani ga bidiyon wanda shafin @seunoloketuy ya wallafa a Instagram. Mutane da dama sun fusata yayin da suka ce ya zama dole a takawa budurwar da masu irin wannan abun birki.

Mutane da dama sun daura alhakin abun kan yunwa da talauci. Kalli wasu daga cikin martanin a kasa:

@9jahustler ya ce:

“Kuma take dariya. Dole a kamata.”

@abujasextoyshop ya yi martani:

“Wannan ne dalilin da yasa ban aba masu bara a hanya ko kwabo, na gwammaci na je gidan marayu.”

@dymphnacynthia ta ce:

Kara karanta wannan

‘Dan takara Ya Ba Gwamnati Satar Amsar Magance Matsalar ASUU a Kwana 30

“Lagas ba na masu rauni bane, idan za ka iya rayuwa a Lagas, z aka iya rayuwa a koina a duniya.”

Hotunan Sauyawar Yarinyar Da Aka Haifa A Matsayin Zabiya Shekaru Bayan Mahaifinta Ya Gujeta

A wani labarin, wata uwa da ta cika da alfahari ta nuna yadda kyakkyawar diyarta da aka haifa zabiya ta sauya ta kara kyau.

Mahaifiyar yarinyar mai suna Nshai ta ce mahaifin diyar tata ya yi watsi da su lokacin da aka haifi yarinyar. Baya kaunarta saboda an haifeta zabiya.

Sai dai kuma, shekaru bayan nan, yanzu yana roko don ya dawo cikin rayuwarta kuma a matsayin mahaifinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel