Dalar Amurka Ta Kara Birkicewa a Kasuwa Yayin da Aka Fara Kamfe a Najeriya

Dalar Amurka Ta Kara Birkicewa a Kasuwa Yayin da Aka Fara Kamfe a Najeriya

  • Dalar Amurkar da aka saida N718 ko N720 a makon da ya gabata, ta zama N735 a yammacin Laraba
  • Sai da ‘Yan canji suka saye Dala 1 a kan N728, suka saida ta a N735 a Bureau De Change a jiyan nan
  • A makon nan aka soma yakin neman zaben shugaban kasa, wannan bai rasa alaka da farashin

Abuja – Har zuwa yanzu, tattalin arzikin Najeriya yana cigaba da fuskantar kalubale ta fuskar sukurkucewar darajar Naira a kasuwa.

Wani rahoto da muka samu daga Punch, ya tabbatar da cewa darajar Naira ya kara yin kasa a kan Dala a ‘yan makonnin bayan nan.

Kamar yadda muka ji, a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba 2022, abin da aka saida kowace $1 a wasu kasuwannin canjin ya kai N735.

Kara karanta wannan

An fara kamfe: Atiku Ya Dura Abuja, Tinubu Ya Tafi Landan, Peter Obi Ya Dakata Tukun

‘Yan canji na Bureau De Change da ke garuruwan Legas da Abuja sun saida Dalar Amurka ne tsakanin N718 zuwa N720 a makon jiya.

N718 zuwa N735 a kwana 7

Yanzu haka maganar da ake yi, farashin Dala yana yawo tsakanin N728 zuwa N735. Kusan an samu karin N10 zuwa N15 a mako daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bala Usman ‘dan canji ne a kasuwar Amuwo-Odofin da ke Legas, ya shaidawa jaridar cewa ba a saida Dalar Amurka ($1) a kasa da N728.

Naira
Naira na rage daraja Hoto: independent.ng
Asali: UGC

“N728 ne, ba za a iya saida ta kasa da haka ba.”

- Bala Usman

Wani takwaransa, Abubakar Jamiu da ke Zone 4 a birnin tarayya Abuja ya nuna cewa farashin da ake samun Dala a Legas ya ma yi araha.

“Dala tayi tsada, a N730 muke saida ta, babu kari-babu ragi.”

Kara karanta wannan

Wani Sabon Hasashe Ya Tabbatar da Tinubu, Atiku Ba Za Su Lashe Zaben 2023 ba

- Abubakar Jamiu

Farashi ya kara tashi da yamma

Rahoton yace zuwa yammacin jiya, sai da farashin $1 ya kai N735, har a Legas an saida kowace Dala a farashin kafin a rufe kasuwa.

Da kimanin karfe 5:00 na jiya, wani ‘dan canji da ke Lagos Island yace zai saye Dala a kan N728, sai ya saidawa masu nema a kan N735.

Har farkon makon nan, a banki dai abin da ake saida Dalar ba ta wuce N430. Masana suna ta’allaka karyewar Nairar da tsare-tsaren tattali.

An rasa N160 a kwanaki 360

A Satumban 2021, shekara daya kenan, aka ji labari ‘Yan canji suna saida Dalar Amurka a kan sama da N570 a irinsu Legas da Kano.

Idan za a tuna, a kasuwannin BDC na Kano, farashin Dala ya kai N575. Jama'a sun rika sayen Pound Sterling, £1 a kan N780 ne a lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel