Gwamnan CBN ya gagara rike darajar Naira, Dalar Amurka ta lula zuwa N575
- ‘Yan canji suna saida Dalar Amurka a kan sama da N570 a makon nan
- A kasuwannin BDC na Kano, farashin Dala ya kai N575 a ranar Litinin
- Naira ta kuma rasa kimar ta a kan Pound Sterling, £1 ta kai har N780
FCT, Lagos, Kano - Farashin dala ya koma tsakanin N572 zuwa N575 a hannun ‘yan canji. Punch ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 20 a watan Satumba, 2021.
Jaridar tace dalar Amurka tana ta tashi a kasuwar canji duk da babban bankin Najeriya ya dakatar da aikin Aboki Fx da nufin a rage karyewar Naira.
Manema labarai sun ziyarci kasuwar bureau de change na ‘yan canji da ke unguwar Wuse a Abuja, inda suka ga cewa ana saida kowace Dala a Naira 574.
2023: Babban Abin Kunya, Koma Baya Yayin Da Yan Sanda Suka Kama Jigon APC Da PVC Guda 367, An Bayyana Sunansa
A karshen makon jiya, ana canza Dalar Amurka ne a kan N570, hakan na nufin an samu canjin N4.
Rahoton yake cewa ‘yan canjin da ke Legas kuma suna saida Dala ne a kan N572. A Kano abin ya fi kamari, mutane suna sayen Dalar Amurka a kan N575.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Nawa ake canjin Pound Sterling?
Kawo ranar Litinin da kimanin karfe 3:00 na rana, ‘yan kasuwar canji sun saida kudin Pound Sterling na kasar Birtaniya a kan N780, a maimakon N770.
Daga ranar Juma’a da ta wuce zuwa yanzu, Pound Sterling ya kara akalla N10 a kan kudin Najeriya.
Tashin da kudin kasar wajen suka yi zai kara jawo kayan da ake shigo da su daga ketare su kara tsada, a daidai lokacin da ake kukan tsadar kaya a Najeriya.
Rufe Aboki Fx bai yi tasiri ba?
A makon jiya ne gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele, ya zargi kafar Aboki Fx da jawo karyewar Naira da aikin da suke yi na bayyana farashoshi.
Aboki Fx sun musanya wannan zargi, sun ce babu hannunsu a tashin kudin kasar wajen. A cewarsu aikinsu shi ne su sanar da nawa ake yin canjin kudi.
Osinbajo zai dace da mulki
Yayin da ake batun 2023, Kungiyar Progressive Consolidation Group ta fitar da gwaninta, tace Farfesa Yemi Osinbajo ya fi cancanta ya zama Shugaban kasa.
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule yana goyon bayan Progressive Consolidation Group a zabe mai zuwa, yace babu wanda ya kai Osinbajo dace wa da mulki.
Asali: Legit.ng