Kebbi: Motar Dakko Kudi Ta Yi Hatsari, Mutum 6 Har Da Yan Sanda Sun Mutu

Kebbi: Motar Dakko Kudi Ta Yi Hatsari, Mutum 6 Har Da Yan Sanda Sun Mutu

  • Wani mummunan hatsari ya faru a kan babban hanyar Argungu zuwa Birnin Kebbi inda mutane shida suka riga mu gidan gaskiya
  • Abubakar Nafi'u, kakakin yan sandan Kebbi ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce wata mota Carine E dauke da jarkokin man fetur ne ta yi karo da motar dakko kudi
  • Sakamakon hakan, motocci guda biyar da babur guda daya sun kone kurmus sannan wasu mutane shida sun jikkata

Jihar Kebbi - Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutum shida cikin har da yan jami'an sanda uku a hatsarin mota da suka faru a ranar Talata kan hanyar Argungu-Birnin Kebbi a jihar.

Kakakin yan sandan jihar, SP Abubakar Nafi'u, ya bayyana hakan cikin sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Birnin Kebbi, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

An gano wata maboyar 'yan bindiga a Arewa, an fatattaki tsageru, an ceto mutanen da aka sace

Hatsarin Kebbi.
Mutane 6 Sun Mutu A Hatsarin Motar Dakko Kudi A Jihar Kebbi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Hatsarin ya faru ne lokacin da wata Carine E, dauke da jarkokin fetur, da ake zargin jami'an kwastam na suka biyo ta daga Birnin Kebbi.
"Da isarta kauyen Jeda, Carine E din ta yi karo da motar dakko kudi, ta kama da wuta ta kona wasu motoci uku.
"Sakamakon hakan, motocci biyar da babur daya suka kone kurmus.
"Mutane shida ciki har da yan sanda uku sun mutu, yayin da wasu mutum biyar da yan sanda uku suka jikkata kuma an garzaya da su Cibiyar Lafiya na Tarayya, Birnin Kebbi don musu magani."

Kwamishinan yan sandan Kebbi ya yi martani

Nafi'u ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Ahmed Magaji Kontagora, ya ziyarci wurin da hatsarin ya faru.

Ya ce:

"Magaji-Kontagora ya kuma tabbatarwa mutane cewa za a gudanar da sahihin bincike kan yadda lamarin mara dadi ya faru."

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Mummunan hatsarin mota ya laƙume rayukan mutum 15 a Jigawa

A wani rahoton, Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Jigawa ta ce a kalla mutane 15 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Lawan Shiisu, a ranar Litinin a garin Dutse ya ce hatsarin ya faru ne a hanyar Achlafiya zuwa Karnaya, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel