Sojoji Sun Dira a Maboyar ’Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 3, Sun Kwato Makamai da Harsasai a Kaduna

Sojoji Sun Dira a Maboyar ’Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 3, Sun Kwato Makamai da Harsasai a Kaduna

  • 'Yan bindiga sun sha ragargaza a hannun sojojin Najeriya yayin da aka gani maboyarsu a jihar Kaduna
  • An ceto mutum uku da tsageru suka sace, an kuma mika su ga danginsu jim kadan bayan bincike a kansu
  • An kuma kwato wasu makamai da kayayyakin aikata laifuka a maboyar 'yan ta'adda bayan share ta

Kaduna - Jami'an sojin rundunar Operation Forest Sanity sun farmaki maboyar 'yan bindiga a kokarin da suke na kakkabe dazukan Kuriga-Manini-Udawa a hanyar Chikun zuwa Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Laraba 28 ga watan Satumbam Leadership ta ruwaito.

Aruwan ya ce, jami'an tsaron sun yi arba da 'yan bindigan, kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga yayin da sojoji suka fi karfinsu.

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

An ceto mutum 3 daga maboyar 'yan bindiga, an ragargaji tsageru
Sojoji Sun Dira a Maboyar ’Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 3, Sun Kwato Makamai da Harsasai a Kaduna | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Sanarwar ta kuma kara da cewa, an kwato bindiga kirar AK-47, harsasai 18 da kuma wasu makamai 11.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sanarwar:

"A farmakin da aka kai maboyar, rundunar tsaro ta ceto mutum uku da aka yi garkuwa dasu, sune; Luka Ibrahim, Yusuf Jibril da Saminu Abdullahi."

Ta kuma kara da cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta yaba da kwazon soji bisa wannan nasara da suka samu na fattakar 'yan bindiga, haka nan Daily Sun ta ruwaito.

Aruwan ya kara da cewa:

"Wadanda aka ceton tuni an hada su da ahalinsu. Dakaru za su ci gaba da aiki tukuru a dukkan yankunan."

Hakazalika, ya kuma nemi mazauna jihar da su sanar da jami'an tsaro duk wani motsin 'yan ta'adda wadannan lambobin wayan: 9034000060 da 08170189999.

Kotu Ta Daure Basaraken Gargajiya a Legas Tsawon Shekaru 15 a Gidan Yari

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kan Sojojin Najeriya, Sun Tafka Ɓarna

A wnai labarin, wata babban kotun da ke zama a Ikeja ta daure wani basaraken da aka tsige, Bale na Shangisha a Mogodo, Mutiu Ogundare, inda zai zauna a magarkama na shekaru 15, The Nation ta ruwaito.

An kama shi da laifin karyar cewa wasu sun yi garkuwa dashi, lamarin da ya sa kotu ta tasa keyarsa zuwa gidan gyaran hali.

Mai shari'a Hakeem Oshidi ya yankewa Ogundare hukunci ne bayan kama shi da laifuka biyu na tada hankalin jama'a da kuma karyar cewa an yi awon gaba dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel