Mummunan hatsarin mota ya laƙume rayukan mutum 15 a Jigawa

Mummunan hatsarin mota ya laƙume rayukan mutum 15 a Jigawa

  • Mutane guda 15 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota da ta faru a jihar Jigawa
  • Hatsarin ya faru ne tsakanin wasu direbobin motocci kirar Golf guda biyu inda suka yi gaba da gaba kuma motocinsu suka kama da wuta
  • Daya cikin direban da fasinja daya sun kone kurmus yayin da sauran mutanen kuma aka kai su asibiti inda likita ya tabbatar sun mutu

Jigawa - Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Jigawa ta ce a kalla mutane 15 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Lawan Shiisu, a ranar Litinin a garin Dutse ya ce hatsarin ya faru ne a hanyar Achlafiya zuwa Karnaya, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bidiyon yaron da ya ɓoye cikin injin jirgin sama don tsananin son zuwa ƙasar waje, ƴan sanda sun kama shi

Mummunan hatsarin mota ya laƙume rayukan mutum 15 a Jigawa
Taswirar Jihar Jigawa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

ASP Shiisu ya ce motoci biyu ne hatsarin ya ritsa da su misalin karfe 5 na yamma a karamar hukumar Yan Kwashi na jihar.

Ya ce:

"Motoccin biyu sun hadu ne gaba da gaba, sun yi karon ne yayin da daya daga cikinsu ya ke kokarin kaucewa rami a titin.
"Motoccin da hatsarin ya ritsa da su sun hada da Golf mai lamba X1 361 da BCH da wata Golf din mai lamba FST 276 CX.
"Dukkansu motoccin biyu sun kama da wuta, direba daya da fasinja sun kone ta yadda an gasa gane ko wanene."

Shiisu ya ce likita a wani asibiti da ke kusa da inda abin ya faru ya tabbatar da cewa dayan direban mai suna Ashiru da fasinjoji 12 sun mutu, rahoton The Nation.

A cewarsa, ana nan ana cigaba da zurfafa bincike kan musababbin abin da ya haifar da hatsarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun dira gonar wasu mutane yayin da suke girbi, sun tafka aika-aikta

Mutum 9 sun mutu, 41 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Kano

A wani labarin, hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa, FRSC, ta tabbatar da rasuwar mutum 9 sakamakon hatsarin mota da ta faru a Kunar Damawa a ƙaramar hukumar Ɗanbatta a Kano, rahoton PM News.

Da ya ke tabbatar da hatsarin a ranar Lahadi, kwamandan hukumar a Kano, Zubairu Mato, ya ce mutum 41 sun kuma jikkata a hatsarin.

"An kira mu misalin ƙarfe 4.10 na yamma, ranar Lahadi, don haka muka aika jami'an mu cikin gaggawa zuwa inda abin ya faru don ceto wadanda hatsarin ya rutsa da su tare da kawar da abubuwan da ke titin," in ji Mato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel