Majalissar Wakilai Ta Fusata Kan Rashin Karasa Aikin Titin Abuja Zuwa Kano Na N797bn

Majalissar Wakilai Ta Fusata Kan Rashin Karasa Aikin Titin Abuja Zuwa Kano Na N797bn

  • Majalisar wakilai a Najeriya ta bayyana damuwa kan yadda aka gaza kammala aikin titin Abuja zuwa Kano
  • Majalisa ta umarci minista da ya tuntubi kamfanin da ke aikin, kana ya umarce su da su gaggauta kammala aikin
  • An yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da tsaro a titin Abuja zuwa Kaduna domin tabbatar karasa aikin

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta Najeriya ta bukaci ministan ayyuka, Babatunde Fashola da ya gaggauta umartar kamfanin Julius Berger da ya koma bakin aikin kammala aikin titin Abuja-Kaduna-Kano, kuma ya fara daga titin Jere-Kaduna.

Wannan kira na majalisa na zuwa ne bayan da Garba Datti Muhammad da wasu 'yan majalisu 38 suka tado da batun a majalisa, Daily Trust ta ruwaito.

Idan baku manta ba, majalisr zartaswa ta kasa ta sauya kudaden da aikin zai ci a watan Maris din bara, inda ya koma N797.2bn daga N155bn.

Majalisa ta umarci a gaggauta kammala titin Abuja zuwa Kano
Majalissar Wakilai Ta Fusata Kan Rashin Karasa Aikin Titin Abuja Zuwa Kano Na N797bn | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wancan lokacin, ministan ayyuka ya bayyana dalilai da suka sa gwamnati ta kara yawan kudin, duba da yadda hanyar ta kara lalacewa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majalisar ta bayyana cewa, Fashola yace kamfanin na Julius Berger da tun farko aka ba gyaran hanyar zai kuma sake gina ta idan ta fara lalacewa kafin a kammala aikin.

Dalilin dakatar da aikin

Sun ce, bayan yawaitar sace-sace da harin 'yan bindiga a hanyar Abuja zuwa Kaduna, kamfanin ya janye ma'aikatansa a kan hanyar saboda tsaro.

Majalisar ta kuma shaida cewa, kafin kamfanin ya janye ma'aikatansa, tuni aikin ya fara nisa, amma daga baya ruwan sama ya wanke mafi yawan kasa da duwatsun da suka zuba a hanyar.

Da suke koka yanayin hanyar, sun ce hanyar a yanzu ya kai da zarar babbar mota ta yi samu matsala to cunkoso zai hana kowa wucewa, rahoton Tribune Online.

Hakazalika, majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dasa jami'an tsaro da hanyar samar da bayanai domin kamfanin na Julius Berger ya koma bakin aiki tare da kara aikin.

Babu Wata Jiha da Aka Ba Izinin Mallakar Makamai Masu Sarrafa Kansu, Martanin Fadar Buhari Ga Gwamna Akeredolu

A wani labarin, gwamnatin Najeriya ta ce, babu wata jiha a Najeriya da ke da ikon mallakar makamai masu sarrafa kansu kamar dai bindigogi kirar AK47, TheCable ta ruwaito.

Wannan batu na fitowa ne daga wata sanarwa da fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fitar a yau Talata 27 ga watan Satumba.

Gwamnati ta ce, mallakar bindiga kirar AK47 matukar ba a hannun jami'an tsaro bane to tabbas ya saba doka, kuma akwai hukunci a kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel