Gwamnatin Tarayya Ta Ciyo Bashin N1tr Don Biyan Kudin Tallafin Man Fetur Bana

Gwamnatin Tarayya Ta Ciyo Bashin N1tr Don Biyan Kudin Tallafin Man Fetur Bana

  • Gwamnatin Najeriya ta ci bashin bilyan dubu daya bana don biyan tallafi man fetur, cewar DMO
  • Duk da haka gwamnai ta kara farashin man feturin daga N165 zuwa N175 a jihohin Najeriya
  • Ana bin Najeriya bashin $42.8 billion yanzu haka, amma ministar ilimi tace hakan ba abin damuwa bane

Abuja - Gwamnatin tarayya ta karbi bashin N1 trillion domin biyan kudin tallafin man fetur a shekarar nan, Dirakta Janar na ofishin manejin basussuka DMO ta bayyana.

Dirakta Janar, Ms. Patience Oniha, ta bayyana hakan yayin gabatar da lakca kan yin kasafin kudi a Army Resource Centre, dake Abuja, rahoton TheNation.

Oniha tace rashin kudi ne ya tilastawa gwamnati kara cin bashin N1trillion don iya biyan kudin tallafin mai.

Oniha
Gwamnatin Tarayya Ta Ciyo Bashin N1tr Don Biyan Kudin Tallafin Man Fetur Bana Hoto: DMO
Asali: UGC

Duk da ana bin Najeriya bashin $42.8 billion yanzu haka, Ms. Oniha tace ba komai bane, bai da yawa.

Kara karanta wannan

Babu Banbanci Tsakanin Obi, Atiku Da Tinubu, In Ji Kachikwu, Dan Takarar Shugaban Kasa Na ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kara da cewa ana karban bashi ne don yin ayyukan da zasu taimaka wajen samar da aikin yi, sufuri, da inganta tattalin arziki.

Ta ce Najeriya na fama da matsalar karancin kudin shiga, kuma ya zama wajibi gwamnati ta maida hankali wajen samun kudin shiga don rage karban basussuka.

Jakadan Kasar China Ya Yi Magana Kan Kwace Kadarorin Najeriya Idan Ta Gaza Biyan Bashi

A wani labarin kuwa, jakadan kasar Sin zuwa Najeriya, Mr Cui Jianchun, ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa ba ta da niyyar kwace kadarorin Najeriya idan ta gaza biya basussukan da ake binta.

Jianchun ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin ziyarar da wakilin Sin kan lamuran Afrika, Liu Yuxi, ya kaiwa karamin Ministan harkokin wajen Najeriya, Zubairu Dada, a Abuja.

Sun kai masa wannan ziyara ne don karfafa alakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Sin.

Kara karanta wannan

An kama fasto a jihar Arewa bisa bude asibiti a cocinsa, yana ba da maganin bindiga

Ya ce kasar Sin ta yarda da Najeriya kuma ba ta da niyyar kwace kadarorin Najeriya inda aka ki biyan bashin da aka karba don gine-gine.

Asali: Legit.ng

Online view pixel