An Yi Arangama Tsakanin Yan Sanda Da Yan Kalare A Gombe, Wasu Sun Jikkata

An Yi Arangama Tsakanin Yan Sanda Da Yan Kalare A Gombe, Wasu Sun Jikkata

  • Mutane biyu sun jikkata sakakamon arangama da aka yi tsakanin Yan Sanda da Yan Kalare a Jihar Gombe
  • Mahi Mu'azu Abubakar, kakakin yan sandan Jihar Gombe ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce mutanen biyu suna asibiti
  • Kwamishinan yan sandan jihar Ishola Babaita ya gargadi bata gari da kungiyoyi cewa rundunar ba za ta raga wa kowa ba

Gombe - An tabbatar da cewa mutane biyu sun jikkata sakamakon rikici da ya barke tsakanin jami'an yan sandan da yan Kalare a jihar Gombe, The Nation ta rahoto.

Kakakin yan sandan jihar, ASP Mahi Mu'azu Abubakar, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce mutane biyun da suka hada da dan Kalare daya da wata mata da ke wucewa, an kai su Asibitin Koyarwa na Tarayya ta Gombe don magani.

Kara karanta wannan

Akeredolu: Babu Gudu Babu ja da Baya kan Shirin Ba Sojojin Amotekun Makamai

Taswirar Jihar Gombe
An Yi Arangama Tsakanin Yan Sanda Da Yan Kalare A Gombe, Wasu Sun Jikkata. Hoto: @TheNationNews.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda rikicin ya samo asali

Ya ce rikicin ya barke ne a lokacin da wasu gungun yan Kalare kimanin 50 daga Kwala Street Jekadafari Quaters dauke da makamai kamar adda, wuka, sanduna da wasu makamai masu hadari suka tare titin Central Roundabout suka fara kaiwa mutanen gari hari.

A cewarsa:

"Bayan samun kiran neman dauki, tawagarmu sun tafi wurin domin su tarwatsa yan dabar amma hakan bai yiwu ba; domin sun kai wa tawagar hari hakan yasa aka yi amfani da karfi a kansu.
"Sakamakon hakan, daya cikin yan Kalare da wata mata da ke wuce sun samu rauni kuma yanzu ana musu magani a Asibitin Tarayya ta Gombe."

Kwamishinan yan sanda ya gargadi bata gari a Gombe

Kwamishinan yan sanda na Gombe, Ishola Babaita ya gargadi dukkan masu niyyar aikata laifi da kungiyoyin su guji tada hankulan mutanen, kafin, yayin da bayan zabe a jihar.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023

Ya ce duk mutum ko kungiya da aka kama za su fuskanci hukunci dai-dai da doka.

Babaita ya yi kira ga mutanen jihar su cigaba da harkokinsu na halas ba tare da tsoro ko fargaba ba domin rundunar tana binciken gano dukkan bata gari ta gurfanar da su a gaban kotu.

Mutane Da Yawa Sun Jikkata Yayin da Yan Daba Suka Farmaki Wurin Taron LP

A wani rahoton, wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan daban siyasa ne sun kai farmaki tare da tarwatsa taron jam'iyyar Labour Party (LP) ta Peter Obi a ƙaramar hukumar Awgu, jihar Enugu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Maharan, waɗan da suka kai adadin mutum 20, an ce sun mamaye wurin taron ne ɗauke da bindigu da Wuƙaƙe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel