Mutane Da Yawa Sun Jikkata Yayin da Yan Daba Suka Farmaki Wurin Taron LP

Mutane Da Yawa Sun Jikkata Yayin da Yan Daba Suka Farmaki Wurin Taron LP

  • Wasu muatane ɗauke da bindigu da makamai masu haɗari sun tarwatsa wurin taron jam'iyyar Labour Party a jihar Enugu
  • Wani shaida da lamarin ya faru a idonsa ranar Lahadi, ya faɗi yadda maharan suka buɗe wuta, suka jikkata mutane da dama
  • Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, shi ne ɗan takarar shugaban kasa a LP, kuma suna wannan taro ne dominsa

Enugu - Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan daban siyasa ne sun kai farmaki tare da tarwatsa taron jam'iyyar Labour Party (LP) ta Peter Obi a ƙaramar hukumar Awgu, jihar Enugu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Maharan, waɗan da suka kai adadin mutum 20, an ce sun mamaye wurin taron ne ɗauke da bindigu da Wuƙaƙe.

Kara karanta wannan

Hotuna: Lamiɗo, Da Wasu Yan Takarar Gwamna 16 Na Jam'iyar PDP Sun Sa Labule da Wike

Taswirar jihar Enugu.
Mutane Da Yawa Sun Jikkata Yayin da Yan Daba Suka Farmaki Wurin Taron LP Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa harin ya bar mutane aƙalla 17 kwance a Asibiti suna jinyar raunukan da suka ji, kamar yadda Premium Times ta ruwaiato.

Lamarin ya faru a garin Awgu, hedkwatar ƙaramar hukumar Awgu, jihar Enugu ranar Lahadi da misalin ƙarfe 6:00 na yammaci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda lamarin ya faru

Wani shaida da lamarin ya faru a kan idonsa, ya bayyana cewa mutane da yawa sun jikkata yayin da 'yan bindigan suka buɗe wa mambobin jam'iyyar wuta.

Mai Idon Shaidan yace:

"Sun isa wurin taro a cikin Motocin Bas guda biyu kuma muna gab da rufe taron sai suka buɗe wuta a iska."
"Lokacin da masu rike da bindiga suka buɗe wuta a iska, sauran dake rike da adduna da wukake suka farmake mu, suka jikkata mutane da dama."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Bankuna Uku a Jihar Arewa, Sun Kwashi Makudan Kuɗi

Wani rahoto ya nuna cewa ɗaya daga cikin mambobin jam'iyyar, wacce ta shiga motarta domin amsa kiran waya, ta tsallake rijiya da baya yayin da maharan suka harbeta kai tsaye.

Ba'a samu mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ba yayin da aka nemi jin ta bakinsa game da hari.

A wani labarin kuma Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Mayakan Boko Haram sun farmaki al'umman Ngulde da ke karamar hukumar Askira-Uba a jihar Borno.

Mummunan harin da kungiyar ta'addancin ta kai ya yi sanadiyar mutuwar babban limamin Gima da wasu mutane uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel