Akeredolu: Babu Gudu Babu ja da Baya kan Shirin Ba Sojojin Amotekun Makamai

Akeredolu: Babu Gudu Babu ja da Baya kan Shirin Ba Sojojin Amotekun Makamai

  • Gwamna Akeredolu na jihar Ondo yace babu gudu balle ja da baya, sai ya bai wa sojojin Amotekun makamai
  • Ya sanar da cewa, an horar da sabbin jami'an kuma babban abunda zai hana su aiki shi ne rashin wadatattun makamai
  • Gwamnan ya yanke shawarar bai wa Amotekun makamai ne bayan gwamnatin tarayya ta amince da bai wa 'yan sandan yanki na Katsina

Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya ce babu gudu babu ja da baya kan matakin da gwamnatinsa ta dauka na siyo makamai da alburusai tare da rarrabe su ga jami’an tsaron jihar, Amotekun.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Akeredolu ya bayyana cewa, makaman da jihar za ta tallafa, za a yi amfani da su ne wajen yakar wadanda ya kira ‘yan daba masu aikata laifukan cin zarafi da zaluncin bil’adama.

Kara karanta wannan

Bauchi: Raba Mata Da Maza A Makarantun Sakandare Ya Harzuka Dalibai, Sun Mamaye Tituna Suna Zanga-Zanga

Gwamna Akeredolu
Akeredolu: Babu Gudu babu ja da Baya kan Shirin Ba Sojojin Amotekun Makamai. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya ce dole ne a yi amfani da karfin ikon jihar wurin yaki da masu tada hankali da masu rike da makamai wadanda ba hukuma ba

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin a wajen rantsuwar sabbin ma’aikatan Amotekun da aka dauka a Akure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akeredolu ya ce kafa hukumomin tsaro da wasu jihohi suka yi ya zama dole kuma babu makawa.

A Kalamansa:

“Dole ne a baiwa rundunar Amotekun kayan aikin da za ta gudanar da muhimman ayyukanta na tsaro a halin yanzu.
“Tun shekaru aru-aru, an yi mana gargaɗi cewa rashin kayan aiki ke kawo gazawar ma'aikata. Game da sojojin Amotekun, ana sa ran ma’aikata zasu yi aiki ba tare da kayan aiki masu kyau ba.
“Wadanda aka rantsar a yau sun samu horo mai tsauri wanda jihar ta dauka nauyi. Horon ba zai ƙare a nan ba, zai ci gaba. "

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Wasu Manyan Gwamnonin Arewa 3 Na Shirin Marawa Peter Obi Baya

A makon da ya gabata ne gwamnan ya yanke shawarar siyan makamai don amfanin jami’an Amotekun bayan wani faifan bidiyo da ya nuna amincewar gwamnatin tarayya na ba da makamai a jihar Katsina.

Ya kuma kara da cewa, ba daidai ba ne a bar tsageru, musamman a yankin Neja-Delta, su rike nagartattun makamai yayin da aka hana jami’an jiha.

Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Sheke Manoma 3, Sun yi Garkuwa da Wasu 22

A wani labari na daban, wasu ‘yan bindiga da suka kai farmaki a wasu kauyukan karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna sun halaka a kalla mutane uku.

Channels TV ta rahoto cewa, an ce wadanda harin ya ritsa da su manoma ne da ke aiki a gonakinsu ranar Asabar lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmakin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel