Wasu Na Kishi: Matashi Ya Jinjinawa Matarsa Yayin da Take Girki Da Icce A Bidiyo

Wasu Na Kishi: Matashi Ya Jinjinawa Matarsa Yayin da Take Girki Da Icce A Bidiyo

  • Wani magidanci da matarsa sun burge mutane da dama da salonm soyayyarsu a kan TikTok yayin da mijin ya jinjinawa masoyiyar tasa
  • Da yake tayata girki a madafi, matashin ya yi ihun ‘matata’ don nunawa mutane irin kyawu da matar ke da shi
  • Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka kalli bidiyonsu sun bayyana cewa su dukkansu suna da kyau kuma gasu matasa

Wasu ma’aurata da suka daura bidiyoyi a TikTok sun haifar da zafafan martani yayin da mijin ya jinjinawa matar tasa a madafi yayin da take girka masu abinci.

Yayin da take girki a kan icce, mijin na ta ihun ‘matata’. Bayan ya yi wannan firucin, ya jaddada kalamunsa na farko yayin da yake kara kuwa.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Na Fama Da Matsanancin Yunwa Ta Yadda Basa La'akari Da Addinansu A Zaben 2023 - Keyamo

Mata da miji
Wasu Na Kishi: Matashi Ya Jinjinawa Matarsa Yayin da Take Girki Da Icce A Bidiyo Hoto: TikTok/@zhengeraldjr
Asali: UGC

Yayin da mijin ke jinjina mata, matar ta kalli kamaran cike da mamaki sannan ta dandana abun da take gikawa.

Masu amfani da TikTok da dama da suka kalli bidiyon sun bayyana cewa sun ce sun burgesu sannan cewa su dukka biyun suna da matukar kyau gashi mutumin na nunawa duniya ita ba tare da yaji kunya ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

Leroy Sane Jr @19 ya ce:

"wasu matan sun fara kishi, kai miji nagari ne dan uwa ina alfahari da matarka,,,harma da wallafar."

Beib j fatma ta ce:

"Mutane na da sa'a a wajen nan."

user2846984401212 ya ce:

"Na so yadda kake alfahari da kyakkyawar matarka."

miss.nakhanya ta ce:

"Kun dace da junanku."

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka

Secretary team byononese ta ce:

"Gaskiya ne mutum ya auri abokinsa."

A Shirye Nake Idan Na Samu Miji Zan Yi Aure: Tsohuwa Mai Shekaru 70 Tace Tana Neman Saurayi

A wani labarin, Alphonsine Tawara ta bayyana cewa har yanzu bata da saurayi kuma ita din budurwa ce sabuwa dal a leda duk da kasancewar ta yi shekaru 70 a duniya.

Matar, wacce ta fito daga kasar Kongo, ta bayyana cewa ta sadaukar da rayuwarta don ceto kannenta sannan cewa za ta yi aure idan ta samu miji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel