A Shirye Nake Idan Na Samu Miji Zan Yi Aure: Tsohuwa Mai Shekaru 70 Tace Tana Neman Saurayi

A Shirye Nake Idan Na Samu Miji Zan Yi Aure: Tsohuwa Mai Shekaru 70 Tace Tana Neman Saurayi

  • Wata tsohuwa mai shekaru 70, Alphonsine Tawara, na burin samun masoyi tare da dandana zumar aure kafin ta mutu
  • Dattijuwar malamar ta ce a shirye take ta amarce idan ta samu masoyin da za ta karasa rayuwarta da shi
  • Alphonsine ta bayyana cewa ta ki yarda da mazaje da dama da suka so aurenta saboda ta mayar da hankali wajen karantar da kannenta

Alphonsine Tawara ta bayyana cewa har yanzu bata da saurayi kuma ita din budurwa ce sabuwa dal a leda duk da kasancewar ta yi shekaru 70 a duniya.

Tsohuwa
A Shirye Nake Idan Na Samu Miji Zan Yi Aure: Tsohuwa Mai Shekaru 70 Tace Tana Neman Saurayi Hoto: Afrimax
Asali: UGC

Tsohuwa ta shirya yin aure

Matar, wacce ta fito daga kasar Kongo, ta bayyana cewa ta sadaukar da rayuwarta don ceto kannenta sannan cewa za ta yi aure idan ta samu miji.

Da take zantawa da AfriMax, ta ce:

Kara karanta wannan

Dole Ka Tattara Komatsanka Ka Koma Najeriya: 'Yar Amurka Da Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta, Bidiyon Ya Yadu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Dalilin da yasa har yanzu banyi aure ba shine ban samu namijin da ya dace dani ba. Amma a lokacin da nake matashiyar budurwa, maza da dama suna ta bibiyata.
Nayi soyayya da dama amma na ki yin aure kafin kannena su kammala karatu saboda ni ke kula da su.”

Alphonsine ta ce ta tsaya har dukka kannenta su kammala karatu amma bata taki sa’a ba…

Ta ce:

“Maza za su tunkareni da batun aure amma sai na ce masu a’a saboda na so na ilimantar da kannena tukuna, sai nayi aure daga baya.”

Alphonsine ta sadaukar da rayuwarta wajen taimakawa yan uwanta

Matar ta sadaukar da rayuwarta wajen ilimantar da yan uwanta har zuwa tsufanta.

Alphonsine ta kasance malamar makaranta, tayi yawancin aikinta a makarantun darikar katolika.

“Bani da ‘dan kaina amma na kasance uwa ga mutane da dama – yaran da na koyar.”

Kara karanta wannan

Budurwa ta shiga damuwa, ta hada kayataccen biki amma kawayenta suka ki hallara

Tsohuwar wacce bata da aure tana burin fadawa tarkon soyayya kuma ta bayyana cewa a shirye take tayi aure idan ta samu miji.

Ta ce:

“Idan na samu miji, zan yi aure. A shirye nake na zama matar aure kuma na koma gidan mijina da zama.”

Alphonsine ta ce ta kasance mai taka-tsantsan a lokacin da take matashiyar budurwa saboda bata so ta zama uwa ba tare da miji ba. Ta ce tana koran maza.

Malamar ta shawarci yan mata da su kasance masu tsafta kafin aure.

Kalli bidiyon a kasa:

'Dan Najeriya Ya Fallasa Bidiyoyin Tsoffin Yan Matansa 5 A Yanar Gizo, Ya Tada Kura

A wani labarin, wani matashi ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya bayan ya bayyana sunayen tsoffin yan matansa.

Matashin dan Najeriyan ya wallafa bidiyoyin kyawawan yan matan a kan TikTok yayin da ya shiga wani sabon gasa da ke bukatar mutum ya wallafa tsoffin yan matansa 5.

Kara karanta wannan

Duk Masu Zuwa Wurina Kudin Mahaifina Suke So Ba Ni Ba, Diyar Miloniya

Gasar na kuma bukatar wanda zai shige ta ya wallafa abu guda da yayi kewa game da tsoffin yan matan nasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel