Yan Najeriya Na Fama Da Matsanancin Yunwa Ta Yadda Basa La'akari Da Addinansu A Zaben 2023 - Jigon APC

Yan Najeriya Na Fama Da Matsanancin Yunwa Ta Yadda Basa La'akari Da Addinansu A Zaben 2023 - Jigon APC

  • Jigon jam'iyyar APC, Festus Keyamo, ya bayyana babban abun da ya fi damun yan Najeriya kan zaben 2023
  • Keyamo ya ce yan Najeriya sun fi damuwa da matsalar yunwa da ke damunsu fiye da addininsu a zabe mai zuwa
  • Ministan ya bayyana cewa Tinubu zai kawo manufofi da za su kawo sauyi ga halin da ake ciki a Najeriya

Abuja - Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Festus Keyamo, ya ce yan Najeriya na fama da tsananin yunwa da basa la’akari da addininsu a zabin da za su yi a zabe mai zuwa.

Mista Keyamo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talbijin na Channels a daren ranar Lahadi, kan sukar da ke ci gaba da fitowa daga tikitin Musulmi da Musulmi na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya Sun Gaji da Abubuwan da ke Faruwa a Kasar nan, Atiku

Keyamo
Yan Najeriya Na Fama Da Matsanancin Yunwa Ta Yadda Basa La'akari Da Addinansu A Zaben 2023 - Keyamo Hoto: Punch
Asali: Facebook

Jam’iyyar APC ta tsayar da Bola Tinubu, wanda yake Musulmi daga kudu maso yamma da Kashim Shettima, Musulmi daga arewa maso gabas a matsayin yan takararta na shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa.

Duk da sukar da take sha daga kungiyoyi da mabiya addinin kirista, jam’iyyar mai mulki bata janye daga tallata tikitin ba, tana mai cewa lallai hakanm ne mafi alkhairi ga yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jaddada wannan matsayin, Mista Keyamo, ya bayyana cewa yan Najeriya za su so ganin manufofi da zai magance yunwar da suke fama da shi maimakon damuwa da addininsu, Premium Times ta rahoto.

Ya ce:

“Yan Najeriya na yunwa, suna son ganin yadda za a magance wannan yunwar, ba wai yadda za a magance addininsu na Kirista ko Musulunci ba.
“Suna son ganin manufofinmu kan noma da abun da Asiwaju yayi a baya a matsayin gwamnan jihar Lagas, yadda ya inganta Lagas da kuma yadda zai kawo irin wannan manufar a Najeriya gaba daya.”

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023

Mista Keyamo ya kuma yi amfani da damar wajen yin martani ga watsi da tikitin Tinubu/Shettima da kungiyar PNF tayi, The Cable ta rahoto.

Kungiyar kiristancin ta ce babu wasu malamai karkashin inuwarta da suka gana da Tinubu a Abuja a ranar Juma’a. Suma sun yi watsi da tikitin addini guda na jam’iyyar.

Kakakin kwamitin kamfen din na APC ya caccaki PFN kan martanin da tayi game da hukuncin jam’iyyarsa. Ya bayyana cewa PFN bata da hurumin sukar hukuncin da jam'iyyar mai mulki ta yanke.

Ya ce:

"PFN ba mambobin jam'iyyarmu bane. Ya kamata su fita su kada kuri'a a wannan ranar.
"Bai kamata su zo suna ja da hukuncin jam'iyyarmu ba a bainar jama'a. Manufofin fastoci ko aikinsu shine jagorantar mutane zuwa aljanna ba wai jagorantar mutane zuwa Villa ba."

Ya kuma jaddada cewa abun da yake son ji idan yaje coci a ranar Lahadi shine wa'azin sanin Allah ba wai batu kan siyasa ko wanda zai shugabance shi ba.

Kara karanta wannan

Dailin Da Yasa Na Yi Shiru Game da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Saraki Ya Magantu

Shugaban Kasa A 2023: Peter Obi Na Kara Yin Suna Da Karfi, Babban Jigon APC Ya Yi Hasashe Mai Karfi

A wani labarin, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya magantu a kan karfin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ke samu gabannin babban zaben 2023.

Jigon na jam’iyyar APC ya bayyana hakan ne a cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook, yana mai bayyana bunkasar da Peter Obi ya samu a tseren shugabancin kasar a matsayin wani lamari da ke tattare da lauje a cikin nadi.

Ya tabbatar da cewar sunan Obi na tashi cikin sauri kuma yana kara samun karfi yayin da yayi hasashen cewa jam’iyyar LP za ta dare PDP a matsayin babbar jam’iyyar adawar kasar a zaben 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel