Sojojin Najeriya Sun Sheke ’Yan Ta’addan Boko Haram/ISWAP 36, Sun Ceto Mutane 130 a Arewa Maso Gabas

Sojojin Najeriya Sun Sheke ’Yan Ta’addan Boko Haram/ISWAP 36, Sun Ceto Mutane 130 a Arewa Maso Gabas

  • Hedkwatar tsaro ta bayyana yadda jami'an sojoji suka raba 'yan ta'adda da dama da duniya a cikin makwanni biyu
  • An ruwaito cewa, jami'am tsaro sun kwato makamai da kayan abinci da ababen hawa duk dai a hannun 'yan ta'addan
  • Dakurun sojin Najeriya na ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda, musamman a kwanakin nan

Jihar Borno - Hedkwatar tsaro ta Najeriya ya ce dakarun tawagar Operation Hadin Kai ta yi nasarar kawar da 'yan ta'adda sama da 36 a ayyuka daban-daban ta sama a yankin Arewa maso Gabas cikin makwanni biyu.

Daraktan yada labarai na ayyukan soji, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a jawabin nasarorin da jami'an tsaro ke samu a yau Alhamis 22 ga watan Satumba a Abuja.

Sojojin Najeriya sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram
Sojojin Najeriya Sun Sheke ’Yan Ta’addan Boko Haram/ISWAP 36, Sun Ceto Mutane 130 a Arewa Maso Gabas | Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Danmadami ya kuma bayyana cewa, an hallaka kasurguman shugabannin 'yan ta'ddan ISWAP da Boko Haram; Abuja Asiya da Abu Ubaida a aikin, rahoton masanin harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun tarfa 'yan ta'addan Boko Haram, sun hallaka da yawa a jihar Borno

Ya ce an kashe Abu Asiya a yankin Parisu, shi kuwa Abu Ubaida an hallaka shi ne a Sheruri duk dai a dajin Sambisa a kwanakin 12 da 15 ga watan Satumba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangare guda, rundunar ta ce ta ceto mutum 130 a hannun 'yan ta'addan tare da kama 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP 46 da kuma abokan harkallarsu 12.

Abubuwan da aka kwato

An kwato bindigogin AK47 guda 21 da alburusai 163 masu girman 7.6mm, bindigogin RPG guda biyu, wasu nau'in bindigogi 25 kayan fashe guda hudu, tirken tasken rana 10, keke 23, babura 10 da keke napep daya.

Hakazalika, an kwato wayoyin hannu 19, fitilu 28 buhunnan hatsi, dabbobi 122 da tsabar kudi N203,125.

A jumillance, hukumar tsaro ta ce akwai mutum 368 cikin 'yan ta'addan da suka mika wuta, ciki har da yara, mata da manyan maza.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP: An kashe 'yan jiha ta 5000 cikin shekaru 11 a hare-haren 'yan bindiga

Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Ta'addan Boko Haram Kwanton Bauna, Sun Kashe Tsageru 7 A Borno

A wani labarin, jami'an sojojin Operation Hadin Kai sun tarfa tawagar 'yan ta'addan da ake zargin 'yan Boko Haram a karamar hukumar Jere ta jihar Borno, an kashe shida yayin da daya ya tsira da raunin harbin bindiga.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a kauyen Kyamla na karamar hukumar, kuma an kwato wasu kayayyakin aikata ta'addanci daga hannun tsagerun.

Wata majiyar tsaro ta shaida cewa, jami'an sun samu bayanan sirri ne da ya kai ga ragargazar wadannan 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel