Kungiyar ASUU Ta Maida Martani Kan Umarnin Kotu Na Janye Yajin Aiki

Kungiyar ASUU Ta Maida Martani Kan Umarnin Kotu Na Janye Yajin Aiki

  • Ƙungiyar Malaman jami'o'i ta Najeriya (ASUU) tace ba zata tsaya haka nan ba, zata ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Kotu ta yanke
  • Kotun ma'aikata a ranar Laraban nan, ta umarci ASUU ta maida wuƙarta kube ta janye yajin aikin da take yi yanzu haka
  • Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya roki lakcarori su kwantar da hankilinsu sun fara haɗa lauyoyi

Abuja - Ƙungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta sha alwashin ɗaukaka ƙara game da hukuncin kotun ɗa'ar ma'aikata, wanda ya umarci Malaman jami'a su koma bakin aiki.

Daily Trust ta ruwaito ƙungiyar na cewa tuni ta fara tattara lauyoyi bisa jagorancin sanannen lauya mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Femi Falana (SAN), domin shigar da ƙara a gaba.

Kara karanta wannan

Bayan Su Wike, Wasu Kusoshin Siyasa a Tafiyar Atiku Sun Koma Bayan Tinubu a Zaɓen 2023

Tambarin ASUU.
Kungiyar ASUU Ta Maida Martani Kan Umarnin Kotu Na Janye Yajin Aiki Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Shugaban ASUU na shiyyar jihar Legas, Adelaja Odukoya, a wata sanarwa da ya fitar bayan Kotu ta yanke hukunci, ya roki mambobin ƙungiyar su kwantar da hankulansu kuma su ɗaura ɗamarar yaƙi har karshe.

Kowa ya kwantar da hankalinsa - ASUU

A sanarwan mai taken, "Umarcin Kotun NICN na ASUU ta koma aiki; Ku kwantar da hankalinku."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ruwayar Vanguard, An jiyo shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, a cikin sanarwan yana mai rokon fusatattun lakcarori su kwantar da hankalinsu, babu wani abun damuwa kan umarnin su koma aiki.

"Ya kamata Mambobin mu su kasance a shirye su haɗa kai. Duk mutanen da kansu a haɗe yake babu mai yin nasara a kansu." inji Osodoke.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa ASUU ta tsunduma yajin aiki ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu, 2022 domin neman a cika mata bukatunta, wanda ya haɗa da tsarin biyan Lakcarori albashi na UTAS.

Kara karanta wannan

2023: Dole Mu Tabbatar da Najeriya Gabanin Shugaban Kasa, Jonathan

A wani labarin kuma kungiyar ɗaliban jami'o'in Najeriya ta yi watsi da hukuncin Kotu wanda ya umarci ASUU ta janye yajin aiki

Daliban sun bayyana umarnin kotun a matsayin wata yaudara, inda suka ce gwamnati ta gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.

A fahimtar daliban, kotu ba ta da hukumin kiran malamai su koma bakin aiki yayin da ta gaza umartar gwamnati ta biya malaman hakkokinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel