Bayan Su Wike, Wasu Kusoshin Siyasa a Tafiyar Atiku Sun Goyi Bayan Tinubu a 2023

Bayan Su Wike, Wasu Kusoshin Siyasa a Tafiyar Atiku Sun Goyi Bayan Tinubu a 2023

  • Jam'iyyar PDM, wacce marigayi Shehu Musa Yar'adua ya kafa daga baya ta koma tafiyar siyasar Atiku, ta yi watsi da tsohon mataimakin shugaban
  • Jam'iyyar wacce aka rushe ta ayyana goyon bayanta ga Tinubu na APC tare da wasu ƙungiyoyi, sun ce shi ya fi dacewa da shugabanci
  • Shugaban PDM na ƙasa, Frank Igwebuike, yace duk da soke musu rijista a 2023, har yanzun tana da rassa a dukkan jihohi 36 da Abuja

Abuja - Aƙalla ƙungiyoyi uku, ciki har da mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Movement (PDM) sun ayyana goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Tinubu.

Bayan PDM, sauran sune ƙungiyar matasa Musulmai da Kiristoci da kuma ƙungiyar dattawa masu son shugabanci nagari (GGG), duk sun mara wa Tinubu baya a zaɓen 2023, kamar yadda thenation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Jam’iyyar Atiku Ta Juya Masa Baya, Za Tayi Wa Tinubu Aiki a Zaben 2023

Bola Tinubu da Atiku Abubakar.
Bayan Su Wike, Wasu Kusoshin Siyasa a Tafiyar Atiku Sun Goyi Bayan Tinubu a 2023 Hoto: Bola Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Shin Atiku ya kafa PDM?

Marigayi Manjo Janar Shehu Musa Yar'adua mai ritaya, shi ne ya kafa jam'iyyar PDM a shekarar 1994, daga bisani ta zama cikakkiyar jam'iyya mai rijista a watan Agusta, 2003.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bugu ɗa ƙari, PDM ta koma tafiyar siyasar Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaɓe mai zuwa.

A 2022, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta soke rijistar jam'iyyar tare da wasu jam'iyyun siyasa da dama.

Rassa nawa PDM gare ta bayan ta zama tafiyar Atiku?

Da yake hira da 'yan jarida ranar Talata 20 ga watan Satumba, shugaban tafiyar na ƙasa, Frank Igwebuike, tare da Sakatariya ta ƙasa, Maimunat Ahmad, yace PDM na da ofisoshin jihohi 36 da birnin tarayya Abuja.

Ya ƙara da cewa tawagarsu ta zauna ta yi karatun natsuwa da nazari kan siyasar Najeriya, amma wanda ta gano ya dace kuma zai iya shi ne Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Allah Ya Yi Wa Wani Shugaban Jam'iyyar APC Rasuwa

A kalamansa yace:

"A lokaci irin wannan, mutane masu kima ne kaɗai za'a kira su taimaka ta hanyar samar da kyakkyawan shugabanci da kare muradan mu."

A wani labarin kuma Gwamnan Arewa Ya Karɓi Ɗaruruwan Masu Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC Ciki Har da Ɗan Takarar Gwamna

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karɓi ɗaruruwan masu sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Daga cikinsu har da ɗan takarar da ya nemi tikitin gwamna a PDP, Abba Gana Tata, Buni ya nuna jin daɗinsa da sauya sheƙar jigon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel