Dalibai Sun Tubure Bayan da Aka Umarci Kungiyar ASUU Ta Koma Bakin Aiki

Dalibai Sun Tubure Bayan da Aka Umarci Kungiyar ASUU Ta Koma Bakin Aiki

  • Daliban Najeriya sun yi watsi da batun umarnin da kotu ta ba ASUU na komawa bakin aiki tare da katse yajin aiki
  • Daliban sun bayyana umarnin kotun a matsayin wata yaudara, inda suka ce gwamnati ta gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyanta
  • A fahimtar daliban, kotu ba ta da hukumin kiran malamai su koma bakin aiki yayin da ta gaza umartar gwamnati ta biya malaman hakkokinsu

Kungiyar daliban Najeriya ta kasa (NANS) ta yi watsi da hukuncin kotu na umartar kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta koma bakin aiki, rahotom jaridar Punch.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta kungiyar, Giwa Yisa Temitope ta ce, sam wannan kira ba komau bane face yanke hukunci kan rashin adalci da daidaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin FG da ASUU, Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki

Daliban Najeriya sun yi watsi da umarnin da kotu ta ba ASUU
Dalibai Sun Tubure Bayan da Aka Umarci Kungiyar ASUU Ta Koma Bakin Aiki | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Hakazalika, kungiyar ta ce tun farko ma bai kamata gwamnati ta maka kungiyar malamansu a kotun ma'aikata ba.

A bangare guda, kungiyar ta ce sam gwamnatin Buhari bata iya shawo kan rikicin da ke iya tasowa ba a kowane lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Kuma muna son bayyanawa karara cewa, ba zai yiwu kotu ta umarci ASUU ta koma ajujuwan karatu ba."

Mafita kawai gwamnati ta ba ASUU kudin da take bukata

A yankin sanarwar, daliban sun ja hankalin kotu da cewa, wannan umarni ba daidai bane, kuma hakan bai warware matsalolin da ke tsakanin ASUU da gwamnati ba.

A cewar sanarwar:

"Kuma, kamar yadda muka gani a yau, tare da hukuncin kotu, mun gane kotu bata wani warware matsalar da ake fuskanta ba kuma mun yi watsi da hukuncin da kakkausar murya.
"Da kamata ya yi kotun ta ce gwamnatin tarayya ta biya a madadin tace lakcarorin da ke cikin yajin aiki su koma ajujuwa."

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan China a Kano ta yi martani kan kisan da dan China ya yiwa budurwarsa a Kano

Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin FG da ASUU, Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki

A wani labarin, labari da ke zuwa mana daga jaridar The Cable shine cewa kotun masana'antu ta Najeriya (NICN) ta umurci kungiyar malaman jami’a wato ASUU da ta janye yajin aikinta da ke gudana a fadin kasar.

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki don ganin gwamnatin tarayya ta biya mata bukatunta ciki harda duba albashin malaman jami’a.

An yi tattaunawa da dama tsakanin malaman ASUU da gwamnatin tarayya amma duk sai a tashi ba tare da an cimma matsaya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel