ICPC: Yadda Ma’aikatan Gwamnati Suka Tafka Cuwa-cuwar N400bn a kasafin kudi

ICPC: Yadda Ma’aikatan Gwamnati Suka Tafka Cuwa-cuwar N400bn a kasafin kudi

  • Wasu ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyi sun cusa kwangilolin bogi a kasafin shekarar 2021 da 2022
  • Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye ya tona wannan asiri da ya ziyarci majalisar datttawa
  • Bolaji Owasanoye yace bayan kwangilolin karya na N300bn, an nemi a ci albashin bogin kusan N50bn

Abuja - Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya tace an cusa mai-men ayyuka na Naira biliyan 300 a kasafin kudin 2021 da 2022.

A ranar Alhamis, 15 ga watan Satumba 2022, Daily Trust ta rahoto shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye yana wannan bayani a majalisar tarayya.

Farfesa Bolaji Owasanoye ya gana da kwamitin kudi na majalisar tarayya yayin da ake kokarin karasa aiki a kan kundin kasafin kudin shekarar badi.

Kara karanta wannan

Sanatoci Za Su Kashe Ma’aikatu, Cibiyoyi da Hukumomin Gwamnati 400 a shekarar 2023

Bolaji Owasanoye ya shaidawa kwamitin Sanatocin cewa hukumomin gwamnati sun maimaita kwangilolin N300bn a kasafin kudin shekarar 2021.

Abin bai tsaya nan ba, an yi cushen Naira biliyan 100 a cikin kasafin shekarar bana. Diddikin ICPC ya bankado yadda ma’aikatan suke facakar biliyoyi.

Su wanene ke wannan aiki?

Rahoton da muka samu yace shugaban hukumar bai tona hukumomin da ke wannan aika-aika ba. Farfesan yace kokarinsu ya ceci gwamnatin tarayya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majalisar Dattawa
Zaman Majalisar Dattawa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

ICPC za ta tattara sunayen wadanda suka yi wannan, ta aikawa kwamtin majalisar daga baya.

Albashin ma'aikatan bogi

Baya ga badakalar kwangiloli, an fahomci cewa wasu hukumomi da ma’aikatun tarayya sun yi yunkurin kashe N49.9bn da sunan albashi a shekarar nan.

Business Day tace an yi nufin batar da makudan kudin nan ne a Junairu da Yunin 2022. ICPC tayi nasara wajen hana a turawa ma’aikatun wadannan kudi.

Kara karanta wannan

Watan Okotba Shugaba Buhari Zai Gabatar Da Kasafin Kudin 2023, Kakakin Majalisa

Shugaban ICPC na kasa ya yi kira ga kwamitocin majalisa da su zura ido da kyau idan an kawo kundin kasafin kudin 2023 domin bankado cuwa-cuwa.

Majalisa ta ji dadin aikin ICPC

Sanata Solomon Olamilekan wanda shi ne shugaban wannan kwamiti, ya ji dadin ayyukan da ICPC take yi, ya yi alkawarin za a kara masu kudin kashewa.

Solomon Olamilekan yake cewa za a kara kasafin kudin hukumar zuwa N1.8bn a shekarar 2023 domin a rika gano rashin gaskiyar da ake yi a MDAs.

An kama 'Yan Yahoo

Kwanaki aka ji yadda jami’an EFCC suka yi ram da wasu da ake zargin ‘Yan Yahoo-Yahoo ne a jihar Kwara, a makon nan aka gama shari’a da wasunsu.

Labari ya zo mana jiya cewa Alkalin kotun tarayya na Ilorin ya yi hukunci, Samuel Onojah, Victor Kadiyamo da Jejelowo Segun za suyi shekaru 20 a daure.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Abubuwan da Zan Yi a Kwanaki 100 na Farko da Zan Yi a Ofis

Asali: Legit.ng

Online view pixel