Watan Okotba Shugaba Buhari Zai Gabatar Da Kasafin Kudin 2023, Gbajabiamila

Watan Okotba Shugaba Buhari Zai Gabatar Da Kasafin Kudin 2023, Gbajabiamila

  • Saura makonni uku kacal shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2023
  • Wannan itace kasafin kudi ta karshe da Buhari zai gabatar matsayin shugaban kasar Najeriya
  • Ministar Kudi tace gwamnati ba zata biyan kudin tallafin mai na shekarar 2023 gaba daya ba

Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2023 gaban majalisar dokokin tarayya a makon farko na watan Oktoba, Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

TheNation ta ruwaito cewa Gbajabiamila ya laburta hakan ne ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

Yayin amsa tambayoyin yan jarida lokacin da ya kai ziyarar ganin ido aikin gyaran da ake yiwa zauren majalisar, Gbajabiamila ya yi gum kan yadda Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudi tunda ana gyara a majalisar.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari

A baya an kasance ana amfani da zauren majalisar wakilai wajen karban bakuncin Shugaban kasa.

Amma kawo ranar Laraba, babu alamun za'a kammala aikin nan da watanni shida.

Gbaja Buhari
Watan Okotba Shugaba Buhari Zai Gabatar Da Kasafin Kudin 2023, Gbajabiamila
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gbajabiamila ya yi kira da ma'aikatan su gaggauta kammala aikin nan da Agustan 2023 kamar yadda sukayi alkawari.

Ga dukkan alamu sai an kammala zaben 2023 za'a iya amfani da majalisar.

A cewarsa:

"Za'a kammala aikin gaba daya a Agustan shekara mai zuwa; saboda hakan kimanin shekara daya kenan."

An tattaro cewa yayinda yan majalisar zasu kammala hutunsu mako mai zuwa, za'a rike amfani da dakin taro na 208 da 231 wajen zaman majalisa.

Majalisar wakilai na da mambobi 360.

Zamu Karbi Sabon Bashin N11tr Kuma Zamu Sayar Da Wasu Dukiyoyin Gwamnati A Shekarar 2023, Minista Zainab

A wani labarin, Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata karbi sabon bashin sama da N11 trillion tare da sayar da dukiyoyin gwamnati don kasafin kudin 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Na Daf da Asarar Naira Tiriliyan 7.58 Yayin da Ake Ƙarma-Ƙarma

Ta bayyana cewa gwamnati zata bukaci kudi N12.42 Trillion idan har zata cigaba da biyar tallafin mai a 2023.

Hajiya Zainab ta bayyana hakan ne ranar Litnin yayinda ta bayyana gaban yan majalsar wakilai

Asali: Legit.ng

Online view pixel