Hotunan Yadda Masu Ababen Hawa Suka Sharbi Kuka Lokacin Da Ake Gwanjon Motoccinsu A Legas

Hotunan Yadda Masu Ababen Hawa Suka Sharbi Kuka Lokacin Da Ake Gwanjon Motoccinsu A Legas

  • Hukumar kula da cinkoson ababen hawa na Jihar Legas ta yi gwanjon ababen hawa da ta kwace daga hannun masu saba dokokin tuki
  • Mutane da dama sun yi halarci wurin da aka yi gwanjon motoccin iri daban-daban ciki har da masu motoccin inda wasu cikinsu suka rika sharbar kuka
  • Mai magana da yawun hukumar ta Legas ya ce an gurfanar da wadanda ke da motoccin a kotu kuma kotu ta bada umurnin gwamnati ta kwace ta sayar da su

Legas - Masu saba dokokin tuki sun tsuguna da gwiwoyinsu, wasu daga cikinsu sun fashe da kuka suna zubar da hawaye yayin gwanjon motoccin da gwamnatin Legas ta kwace daga hannun masu saba dokokin hanya, The Cable ra rahoto.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Aka Fallasa Wata Budurwa Da Ke Bara Da Jinjirin Karya A Lagas

A yayin wurin gwanjon motoccin da aka kwace kuma masu shi ba su karba ba da aka yi ranar Alhamis a harabar hukumar kula da ababen hawa na Legas, masu tayi sun yi tururuwa zuwa wurin domin yin rajista, dubawa tare da tayi ababen hawa daban-daban da suka hada da kananan bus da motocci.

Gwanjon Motocci
Jami'in tsaro yayin jawabi wurin gwanjon motocci a Legas. Hoto: Ibrahim Mansur/thecableng
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwanjon Motocci
Allon gabatar da motoccin da ake gwanjonsu. Hoto: Ibrahim Mansur/thecableng
Asali: Twitter

Auction Lagos
Mahalarta taron wurin da aka yi gwanjon motocci a Legas. Hoto: Ibrahim Mansur/TheCable.
Asali: Twitter

A wurin taron, inda mahalarta suka taru tamkar wadanda suka zo kallon wasan kwallon kafa, ainihin masu ababen hawan sun rika zubar da hawaye suna neman a tausaya musu duba da cewa suna iya rasa abin hawansu har abada.

A cewar shugaban hukumar kula da cinkoson ababen hawa na Legas, CSP Sola Jejeloye, ta bakin kakakin hukumar, PAO, Mr Raheem Ggbadeyanka, hukumar ta kama motoccin ne saboda saba dokokin tuki, musamman satar hanya.

Daga bisani kotun majistare, bayan yin shari'a, ta kwace motoccin ta mika su ga gwamnati domin a yi gwanjonsu, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sokoto: Yan Bindiga Sun Kai Hari Wani Gari Sun Sace Kayan Abinci

An sayar wa wadanda suka fi yin tayi mai tsoka.

Cikinsu har da wata mahaifiya da ta taho tare da danta ta rika roko suna neman a tausaya musu kada a siya motarsu.

Ga dai wasu daga cikin motoccin da aka yi gwanjonsu:

Auction Lagos
Masu tayin motoccin suna daga hannaye yayin da ake gwanjon motoccin a Legas. Hoto: Ibrahim Mansur/@TheCableng
Asali: Twitter

Auction Lagos
Dandazon mutane da suka halarci filin da aka yi gwanjon ababen hawa a Legas. Hoto: Ibrahim Mansur/@TheCableng
Asali: Twitter

Auction Lagos
Mutane da suka halarci wurin gwanjon motoccin a Legas. Hoto: Ibrahim Mansur/@TheCableng
Asali: Twitter

Auction Lagos
Wasu cikin masu motocci suna rokon alfarma. Hoto: Ibrahim Mansur/@thecableng
Asali: Twitter

Auction Lagos
Hotunan Yadda Masu Ababen Hawa Suka Rika Zubar Da Hawaye Lokacin A Ake Gwanjon Motoccinsu A Legas. Hoto: Ibrahim Mansur/thecableng
Asali: Twitter

Auction Lagos
Hotunan motoccin da aka yi gwanjon su a Legas. Hoto: Ibrahim Mansur/thecableng
Asali: Twitter

Auction Lagos
Motoccin da hukuma ta yi gwanjonsu a Legas. Hoto: Ibrahim Mansur/thecableng
Asali: Twitter

Gwanjon Motocci
Motoccin da aka yi gwanjonsu a Legas. Hoto: Ibrahim Mansur/thecableng
Asali: Twitter

Gwanjon Motocci
Ababen hawa da aka yi gwanjonsu a Legas. Hoto: Ibrahim Mansur/thecableng
Asali: Twitter

Bidiyon Wata Kyakyawar Budurwa Mara Hannaye Tana Tuka Mota A Babban Titi Da Kafafunta Dauki Hankulan Mutane

A wani rahoton, a maimakon damuwa da abubuwan da ba za ta iya yi ba saboda rashin hanaye, wata mata mai bukata ta musamman ta kayatar da mutane da abubuwan da ta ke iya yi da kafatunta.

Matar, mara hannaye ta samu mabiya sosai a shafin TikTok inda ta wallafa bidiyon abubuwan da ta ke yi da kafafunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel