Bidiyon Wata Kyakyawar Budurwa Mara Hannaye Tana Tuka Mota A Babban Titi Da Kafafunta Dauki Hankulan Mutane

Bidiyon Wata Kyakyawar Budurwa Mara Hannaye Tana Tuka Mota A Babban Titi Da Kafafunta Dauki Hankulan Mutane

  • Wata mata mara hannaye ta karfafawa mutane gwiwa a dandalin sada zumunta saboda rashin karayarta a rayuwa duk da nakasu ta ke da shi
  • Kyakyawar matar ta wallafa wani bidiyo a dandalin sada zumunta inda ta tuka mota da kafafunta a titi da motocci ke zirga-zirga sosai
  • Ta dora kafarta na dama a kan birki kuma ta rika juya sitiyari da kafarta na hagu wanda ya bawa masu amfani da intanet sha'awa

A maimakon damuwa da abubuwan da ba za ta iya yi ba saboda rashin hanaye, wata mata mai bukata ta musamman ta kayatar da mutane da abubuwan da ta ke iya yi da kafatunta.

Matar, mara hannaye ta samu mabiya sosai a shafin TikTok inda ta wallafa bidiyon abubuwan da ta ke yi da kafafunta.

Kara karanta wannan

Budurwa Tayi wa Banki Fashi Don ta Samu Kudin Maganin Kansar 'Yar Uwarta

Mata mara hannaye.
Bidiyon Wata Kyakyawar Budurwa Mara Hannu Tana Tuka Mota Da Kafafunta Ya Kayyatar. Hoto: TikTok/@itskashmiere1.
Asali: Facebook

A daya daga cikin sabbin bidiyoyinta, matar mai suna @itskashmiere1 ta nuna yadda ta tuka mota da kafafunta.

A yayin da wata mata ce daukan ta bidiyo, matar ta shiga mota ba tare da an taimaka mata ba sannan ta zauna cikin shiri don fara tuki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta dora kafarta na dama a kan birki sannan ta kunna motar da kafarta na hagu. A yayin da kafarta na hagu ke kan birkin, ta rika juya sitiyari da kafarta na hagu.

Bayan matar da ke daukanta bidiyo ta tuna mata batun saka seat belt, ta yi amfani da kafarta ta saka.

Kalli bidiyon a kasa:

Mabanbantan ra'ayoyi kan bidiyon

Jessica George ta ce:

"Da kyau. Idan har za ta iya tuka mota da kafafunta zan iya zuwa in yi koyi tuki don samun lasisi na. Allah ya cigaba da saka mata albarka a duk abin da ta ke yi."

Kara karanta wannan

"Daga Yar Aiki Ta Zama Matan Mai Gida": Budurwa Ta Girgije A Bidiyo Don Farin Ciki

Lorenzo Delisa ta ce:

"Bana ta haufi mace mara hannu za ta iya tuka mota. Kawai ina son sanin yadda ta ke tsarki ne.
"Wannan kam ba ni da haufi ba za ta iya ita kadai ba."

Margie Houston ta ce:

"Baiwa daga Allah. Babu abin da kakarfar mace mai tsoron Allah ba za ta iya ba. Idan akwai niyya, za a cimma nasara. Allah zai cigaba da saka wa bayinsa albarka."

D*ck Moore ya ce:

"Na jinjina mata saboda yin hakan da kula da kanta, a gani na wannan abu ne mai hatsari gare ta da wasu. Babu yadda za a yi ta kaucewa karo da wani motar a lokacin da abin gaggawa ya faru. Abin yabawa ne dai da ta aikata wannan din."

Shaharariyar Jarumar Fina-Finan Indiya Ta Mayar Da Martani Ga Masu Sukar Ta Da Cewa Don Kudi Ta Auri Mijinta

A wani rahoton, kun ji cewa cikin yan kwanakin nan ne aka daura auren shaharariyar jarumar fina-finai na Indiya, Mahalakshmi da furodusa, Ravindar Chandrasekaran.

Kara karanta wannan

Sai Da Aka Kwabe Ni: Wata Budurwa Ta Bayyana Alhininta Na Kulla Soyayya Da Dan Najeriya

Amma, wasu mutane a shafukan sada zumunta sun rika sukar Mahalakshmi kan cewa ta auri Ravinder ne saboda kudinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel