Bayan Mutuwar Mahaifinsu, Wani Ahali a Najeriua Sun Gano an Binne Maciji a Tsakiyar Dakinsa

Bayan Mutuwar Mahaifinsu, Wani Ahali a Najeriua Sun Gano an Binne Maciji a Tsakiyar Dakinsa

  • Wasu iyalai 'yan Najeriya sun kadu yayin da suka gano an binne maciji a turakar mahaifinsu da ya rasu
  • Hotunan mataccen macijin ya yadu a kafar Twitter, lamarin da ya ba mutane da dama mamaki da kaduwa
  • 'Yan Najeriya da dama sun ce ba su yarda haka zai taba faruwa har sai da suka ga irin wannan hoto da 'ya'yan suka yada

Hoton wani mataccen maciji ya yadu a kafar Twitter yayin da wasu ahali 'yan Najeriya suka bayyana gano shi a dakin mahaifinsu.

Abin da ya ba jama'a da dama mamaki shine, mahaifin nasu tuni ya mutu, lamarin da ya kai suka fara zargin macijin na da alaka da mutuwar.

Yadda wasu ahali suka gano an binne maciji a dakin mahaifinsu
Bayan mutuwar mahaifinsu, iyalai sun gano maciji a tsakiyar dakinsa | Hoto: @stephblys and Roger Brooks/w.ang mengmeng/Getty Images
Asali: UGC

A cewar mutumin da ya yada hoton, dama an ba su shawarin su tone daben dakin mahaifin nasu, sai yanzu suka samu damar yin hakan.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Ya kuma bayyana cewa, da yawa daga mutanen da suka zo gaisuwar rasuwa gida, sun yi mafarkin murjejen kumurcin maciji na binsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, ya ce sai da suka tone wurare sama da biyar kafin su iya gano inda macijin yake.

Kafin mu ankara ya rasu

Da yake karin bayani, ya ce sun samu macijin ne a daidai inda mahaifin nasu ke kwance.

A kalamansa:

"Ga mutanen da basu yi imani da irin wannan ba, wannan macijin an samue shi ne a kasan daben dakin mahaifana. Gidanmu ne na kanmu kuma an gyara gidan lokacin da mahaifinmu ya sayi gidan. Abin bakin cikin shine, mahaifinmu ya kwanta rashin lafiya kuma kwatsam ya rasu.

"Wani ya shawarce mu mu tone daidai kasan gadon, nan ne daidai inda mahaifina ke sanya kansa idan zai kwanta. Duk da haka, mun tone wurare sama da 5 kafin mu ga wancan macijin.

Kara karanta wannan

Harin 9/11 Na Amurka: Fasto Adebayo Ya Bayyana Yadda Aka Bincike Shi Saboda Yunkurin Siyan Jirgi

Kalli hoton da rubutun mutumin:

Martanin jama'a

Jama'a sun yi martani bayan ganin wannan hoto mai ban mamaki.

Ga dai abin da suke cewa:

@PentarioDLaw yace:

"Waoh...Allah yasa ya huta. Ta yaya kuka sani kuma har kuka iya tone daben..ku yi hakuri da tambayata...Kawai dai inason sani ne kuma domin wasu su karu."

@ezu_lov yace:

"Lallai wa yaga ina wasa da abu a daidai kaina kamar shirin fim din Nollywood. Wannan lamari babu dadi. Allah yasa ya huta. Muguntar mutane dai bata da iyaka."

@Tommyskizy yace:

"Babbar magana, Allah ya baku hakurin rashi. Nagode Allah da aka gano shi duk da haka, watakila wani ya mutu ta dalilin wannan shirme."

@GbeeXl yace:

"Lallai ya kamata mu dage da addu'a."

Dan Najeriya Ya Tuntsure a Kasa Tsabar Dadi Saboda Matarsa Ta Sauka Lafiya a Asibiti

A wani labarin, wani dan Najeriya ya nuna wani hali mai ban mamaki a asibiti yayin da ya gano matarsa ta haifi jaririnta lafiya.

Kara karanta wannan

Buhari ya magantu, ya ce akwai wadanda ya kamata suke tallata gwamnatinsa amma ba sa yi

Wani bidiyon da @saintavenue_ent1 ya yada a Instagram ya nuna lokacin da mutumin ya shiga asibiti duba matarsa.

Da farko dai gani aka yi mutumin ya durkusa kan gwiwowinsa sannan ya kai kansa ya yi sujudar godiya a kasa. Daga bisani, an ga ya fara birgima a kasa kamar karamin yaro yana dukan kasa da tafukan hannunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel