Bidiyo: Budurwar Da Ta Rabu Da Saurayinta Talaka Saboda Mai Kudi Ta Koka, Bata Auru Ba Bayan Shekaru 10

Bidiyo: Budurwar Da Ta Rabu Da Saurayinta Talaka Saboda Mai Kudi Ta Koka, Bata Auru Ba Bayan Shekaru 10

  • Wata matashiyar budurwa ta wallafa wani bidiyo a TikTok tana mai bayyana yadda ta rabu da saurayinta da suka yi baiko saboda wani mai kudi
  • Sai dai kuma, mai kudin da ta bi bai aureta ba, kuma tsawon shekaru 10 kenan da faruwar abun amma ta kasa auruwa
  • Bayanin nata a TikTok ya haddasa cece-kuce daga jama’a, da dama sun daura laifin a kanta

Wani bidiyo mai tsawon sakanni 56 a TikTok ya nuno wata matashiyar budurwa wacce tace shekarunta 40 amma har yanzu bata da aure.

A cewar budurwar, wani saurayi mai dattako ya nemi aurenta shekaru 10 da suka gabata amma sai daga bisani ta soke shirye-shiryen auren ana saura sati biyu.

Budurwa
Bidiyo: Budurwar Da Ta Rabu Da Saurayinta Talaka Saboda Mai Kudi Ta Koka, Bata Auru Ba Bayan Shekaru 10 Hoto: TikTok/@7menbabymama
Asali: UGC

Ta tuna yadda ta soke auren saboda ta samu wani saurayi mai kudi wanda take tunanin zai aure ta.

Kara karanta wannan

A Raba Aurenmu Don Baya Aikin Komai Sai Jajibe-jajiben Fada, Matar Aure Ta Roki Kotu

Mai kudin ya watsar da ita daga bisani amma dayan saurayin nata da taki aure ya koma kasar waje da zama, ya yi aure kuma yanzu yana da yara uku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar dai yadda yake faruwa a wasan kwaikwayo, har yanzu bata yi aure ba. A daya daga cikin bidiyoyinta, ta ce a yanzu za ta auri koma wanene.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

@wow_704 ta ce:

“Duk muna aikata kura-kurai ba lallai iri day aba amma kuskure kuskure ne.”

@user3210075388412 ta yi martani:

“Ki yarda da Allah, ki yi hakuri da babban darasin da kika koya yar’uwa…ki yafe ma kanki sannan ki ci gaba da harkoki.”

@NHYIRABA3600 ta yi martani:

“Ina ganin ba don dayan yafi kudi bane illa sai dai don ki fi son dayan fiye da wancan, ko?”

Kara karanta wannan

Ruwan dare: Budurwa ta jawo cece-kuce yayin da ta kammala digiri, tace za ta rushe gidansu

@jackyburton531 ta ce:

“Wannan abun bakin ciki ne kuma yana da karfi.”

Matashi Ya Sharbi Kuka Da Hawaye Bayan Ya Gano Cewa An Yi Baikon Budurwarsa Da Wani

A wani labarin, wani dan Najeriya ya fashe da kuka mai tsuma rai bayan ya gano cewa an rigada an yi baikon budurwarsa da wani.

Matashin a cikin wani sakon murya da ke yawo a shafukan soshiyal midiya, ya ba da labarin mawuyacin halin da ya shiga yayin da yake bayyana cewa baida masaniya game da cin amanarsa da take yi.

A cewarsa, ya zata har yanzu suna tare, bai san cewa ta rigada ta shirya amarcewa da wani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel